An Yabawa Gwamna Gaidam  Na Yobe Kan Yadda Ya Ke Kokarin Ciyar Da Harkokin Kiwon Lafiya Gaba

0
89

MUHAMMAD SANI CHINADE, DAGA, DAMATURU

AN yabawa gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam bisa ga kokarin da ya ke yi na ciyar da harkokin kiwon lafiya gaba duk da halin da Jihar ta samu kanta ciki a baya na tabarbarewar harkokin tsaro.

Bayanin haka dai ya fito ne daga bakin shugaban Kwalejin koyon jinya da Ungozoma da ke Nguru Dakta Hamisu Mai Musa ya yin da ya ke karbar lambar yabo kan kwarewar aiki da kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta ba shi.

Shugaban kwalejin ya kara da cewar, ya hakkake cewar gwamnan na nuna matukar kulawarsa kan harkokin na kiwon lafiya inda hakan ne ma ya bashi dawar daga darajar makarantarsu ya zuwa kwaleji don samunkwararrun jami’an kiwon lafiya dai-dai da bukatun Jihar.

Ya kara da cewar, gwamna Gaidam ya wadata makarantar da duk wani kayan aiki da ake bukata hade da samar kayayyakin alatu ga gine-ginenazuzuwa, gidajen malamai, ofisoshi, wuraren gwaje-gwaje da makamantansu, a cewar wannan irin yunkuri ne ya haifar da kwalejin ta samu sahalewar gudanar wassu muhimman kwasa-kwasai akan kiwon lafiya da suka shafi al’umma.

Dakta Hamisu ya ci gaba da cewar cikin irin ayyukan da gwamnan ya yi don daga darajar kwalejin sun hada da sake kwaskware ofisoshin bangaren mulki, dakunan kwana na dalibai, sake gyara manyan zaurukan taruka nakwalejin, sake hada kwalejin da babban layin hasken wutar lantarki ta kasa da kuma samarwa kwalejin manya-manyan injunan samar da hasken wutar lantarki guda biyu tare kuma da samar da wata motar Bus mai daukar mutane 18 da kuma sabuwar motar gudanar ayyuka ga shugaban kwalejin.

Daga nan sai Dakta Hamisu ya ce kwalejin na da shirin samar da wasu karin kwasa-kwasai akalla guda 4 don kara darajar kwalejin kasancewar a halin yanzu tana da kayayyakin aikin da zai kai da a yi hakan.

Tun farko da ya ke jawabi mataimakin babban sakataren kungiyar daliban ta kasa (NANS) Komred Abdulmajeed O. Oyenyi ya ce kungiyarsu ta bada lambar yabo ga shugaban kwalejin ne saboda irin muhimmiyar gudummawar da ya ke bayarwa ne ga harkokin kiwon lafiya a matsayin na kwararre a bangaren na lafiya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.