GWAMNAN JIHAR LEGAS AMBODE YA AMINCE DA SHAN KAYE

0
69

Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNAN Jihar Legas da ke kudancin Yammacin kasar Akinwumi Ambode ya bayyana amincewarsa da shan kayen da ya yi a zaben fitar da Gwanin Jam’iyyar APC domin tsayawa takarar Gwamnan Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas.

Akinwumi Ambode Wanda shi ne Gwamna mai ci a halin yanzu ya bayyana taya mutumin da ake cewa ya kayar da shi wato Baba jide inda ya yi Masa fatar alkairi tare da yin kira ga daukacin al’ummar Jihar Legas da su Goya wa Baba jide baya domin APC ta samu nasarar lashe zaben Gwamna da sauran zabubbukan da za a yi a shekarar 2019 mai zuwa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.