TARZOMA TA BARKE A BUNGUDU TA ZAMFARA

0
75

Mustapha Imrana Abdullahi

RAHOTANNIN da ke fitowa daga garin Bungudu cikin Jihar Zamfara na cewa wadansu matasa sun Kama kone konen Tayoyi a kan Tituna saboda rashin kawo kayan gudanar da zabe da wuri.

Su dai mutanen Bungudu sun koka a kan rashin Kai masu isassun kayan gudanar da zabe, kamar yadda suka ce kuri’ar da aka kawo masu ta yi karanci saboda masu kada kuri’ar sun wuce yawan kayan zaben da aka kawo masu.

Sakamakon wannan tashin tashinar jami’an tsaro sun tarwatsa masu wannan tarzoma domin tabbatar da Doka da oda.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.