Dan Takarar Majalisar Wakilai A Kuros Riba Ya Sha Dakyar A Hannun Masu Zabe

0
82

 

Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba

DAN majalisar dattawa mai wakiltar mazabar kalaba ta kudu a majalisar dattawa Geshom Bassey ya sha dakyar a hannu wasu fusassantun masu zabe a yayin gudanar da zaben fidda gwani.

Fusatattun wakilan yan takara da akaso yi
A ranar laraba ne aka gudanar da zaben a otel din Transcop dake kalaba wanda tun farko an shirya gudanar da zaben ne a filin wasa na UJ Esuene dake kalaba amma aka dawo dashi otel din.
Wakilinmu da ya kasance a harabar otel din a ranar ya ganewa idon sa yadda wakilan masu zaben yan takarar suka watsawa sanata Bassey ruwan Leda a fuska kana wasu kuma na mangarinsa a keya dakyar Jami’an tsaro suka samu.ceton sa daga hannun masu cin zarafin sa.

Dakyar da jibin goshi direban sa ya fita dashi daga wurin a mota yayin da aka kwankwatsa gilasan motar.

Izuwa yanzu da muke kawo muku wannan labarin zaben dai bai gudana ba a ranar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.