Gidauniyar Zakka Da Wakafi Ta Jihar Abiya Ta Tallafawa Wasu Musulmai Mabukata

0
86
PIC.4. NEMA OFFICIAL ADDRESSING SOME INTERNALLY DISPLACED PERSONS (IDPS) IN LAMURDE LOCAL GOVERNMENT AREA OF ADAMAWA STATE ON SATURDAY 19/5/12).

Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba

GIDAUNIYAR zakka da wakafi ta jihar Abiya ta tallafawa wasu daga cikin musulman jihar da kekunan dinki, injinan markade da kuma kudi.
Kudaden sun kama daga naira dubu 25 zuwa dubu 65 domin su dogara da Kansu suyi sana’a.

Da yake raba kayayyakin a Ummuahiya shugaban gidauniyar sulaiman olugunju yace bayar da zakka na daga cikin shika shikan musulunci kuma tausayi da taimako dabi’ace ta musulunci.

Da yake tofa albarkacin bakin sa, kodinetan gidauniyar a jihar Alhaji Suleiman ukandu jaddada mahimmancin fitar da zakka yayi inda yace ” akalla duk mutumin da ya mallaki tsabar kudi da suka kai naira milyan daya da rabi, kamata yayi ya fitar da.zakka.

Alhaji yaro danladi sarkin Hausa-fulani na Ummuahiya, godiya yayi wa gidauniyar a madadin wadanda suka karbi tallafin.

Uwargida Hauwa Yahaya ta shaidawa wakilin mu cewa ” nayi matukar farinciki da samun wannan tallafi na samu abin sana’a da kuma jari” injita

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.