Kamfanin Nmc Ya Ciri Tuta Wajen  Yin Takalma Masu Inganci-Na Mamancy

0
83

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAN kamfanin yin takalma na NMC dake garin Kwa cikin yankin karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Yusuf Na Mamancy yace kamfanin su yayi fice wajen yin ssbbin takalma masu inganci da kyau bisa farashi mai sauki.

Yayi  wannan bayani ne cikin zantawarsu da wakilin mu yayin da ya ziyarci kamfanin a garin Kwa, inda kuma Yusuf NMC ya sanar da cewa dukkanin takalman da ake yi a kamfanin nasu  na zamani ne, sannan  kuma suna da aminci kamar yadda kowane kamfanin yin takalma yake yin nasa.

Haka kuma ya sanar da cewa akwai matasa masu yawa da suke yin aiki a wannan kamfani na NMC  wanda a cewar sa  suna samar da aiyukan yi ga al’uma musamman domin bunkasa dogaro dakai  da kuma magance zaman banza.

Alhaji Yusuf Na Mamancy, ya bayyana cewa suna da abokan hulda masu tarin yawa wadanda suke zuwa sarin kaya wajen su, sannan a  kodayaushe  mutane maza da mata suna tururuwa wajen sayen takalma domin amfanin yau da kullum kamar yadda aka saba.

A karshe, ya bukaci  sauran masu iko da su rika kakkafa kananan masana’antu ta yadda al’uma zasu rika  samun aiyukan yi batare da yawan dogaro da gwamnatoci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.