An Saki Tsohon Shugaban DSS Daura Yayinda Na Kusa Dashi Ke Kokarin Ganin Ya Samu Babban Mukami

0
111

Daga Usman Nasidi

RAHOTANNI sun kawo cewa an saki tsohon shugaban hukumar yan sandan farin kaya, Lawal Daura.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa an saki Daura ranar Talata, 9 ga watan Oktoba sannan kuma cewa wasu na kusa da shi na kokarin ganin ya samu wani babban mukami a gwamnati.

Wata majiya a fadar shugaban kasa a rahoto cewa na kusa da shi na kokarin ganin ya samu mukami mai muhimmanci a tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata majiya ta kuma bayyana cewa: “Wasu mambobin madafi da hukumomi masu karfi a gwamnati na ganin har yanzu ya kamata ace Daura ya samu muhimmin matsayi a kamfen din tazarcen Buhari. “

Wasu sun bayar da shawarar a daukeshi a matsayin kwararre d zai marawa kamfen din baya amma wasu na ganin yaa cancanci komawa matsayinsa a hukumar tsaro kamar yadda yake a 2015.

“Ina ganin zuwa yan makonni masu zuwa za’a shi matsayin da zai hau.”

Hakazalika kamar yadda aka sani Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba ya bayyana Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon darakta janar na hukumar DSS.

Sabon shugaban ya karbi aiki ne daga hannun Mathew Seiyeifa, wanda ya maye gurbin Lawal Daura da aka kora.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.