AN TURA JIRAGEN YAKI JAHAR FILATO

0
88

Rabo Haladu Daga Kaduna

BABBAR magana, wai dan sanda ya ga gawar soja. Wannan magana na nemar tabbata a jahar Filato, inda aka tura sojojin sama da ku,a jiragen yaki saboda ganin yadda rigimar da ake yi, ga dukkan alamu, ta fi karfin ‘yansanda.

Ganin yadda aka yi ta zubar da jini a rikicin jahar Filato, wanda ya ki ci ya ki cinyewa, Rundunar Sojin Saman Najeriya ta tura jiragen yaki da sojoji da kuma wasu kayan yaki don dakile wannan rigimar, wadda ake ganin ta fi karfin ‘yan sanda.

Game da takaddamar da ake yi kan ko ya dace a tura sojoji su yi aikin da a bisa al’ada na ‘yansanda ne, Babban Hafsan Hafsohsin Rundunar SojinSaman Najeriya Air Mashar Sadik Abubakar Yabani ya ce akwai ka’idar

kai sojoji inda ya kamata ace ‘yansanda ne ke kwantar da hankali.

Ya ce an bi wannan ka’idar kafin a yanke shawarar tura sojojin. Haka zalika, wani lauyan kundin tsarin mulkin kasa kuma dan rajin kare hakkin dan adam,

Barrister Yakubu Bawa ya ce idan ta kama ana iya tura soja a wuri mai fama da dadden rikicin da aka kasa shawo kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.