GWAMNONIN APC NA NEMAN A TSIGE OSHIOMHOLE

0
67

Daga Usman Nasidi

WASU gwamnoni a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yi kira ga tsige shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole.

Rahotanni sun bayyana cewa wani minista da yayi Magana kan sharadin boye sunansa a ranar Laraba, 10 ga watan Oktoba ya bayyana cewa basu aminta da tsarin shugabancinsa ba.

Ministan yayi ikirarin cewa gwamnonin basu bayar da komai bat a fannin kudi a babban taron jamiyyar sannan suna tu lura da yadda za’a yi da kudin da aka samu daga siyar da fam.

Ministan ya yi Karin haske cewa wasu gwamoni sun gana da shugaban kaasa Muhammadu Buhari don sanin yadda za’a bi a tsige Oshiomhole.

A baya, majiyarmu ta bada rahoto cewa Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka da za ta magance wadanda ke gujewa biyan haraji ta hanyar tserewa da kudadensu kasashen waje mai suna Voluntary Offshore Assets Regularization Scheme (VOARS).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.