AN KADDAMAR DA KUNGIYAR CI GABAN  KANO TA AREWA  KNDF

0
36

JABIRU A HASSAN, Daga Kano

A RANAR asabar 13 ga Oktoba aka yi bikin kaddamar da kungiyar ci gabam arewacin kano watau” Kano North Development Forun, (KNDF) a  wani kasaitaccen taron da aka yi a babban filin wasa na kwalejin koyar da dabarun noma ta Audu Bako dake Dambatta.

Taron kaddamar da kungiyar ya sami halartar gitattun mutane dake wannan yanki na kano ta arewa musamman wadanda suke zaune a yankin da kuma wadanda suke zaune a wasu sassa na kasar nan domin jaddada goyon bayan su ga kungiyar.

An kuma gudanar da jawabai masu amfani tareda bayyana wasu daga cikin manufofin kungiyar ta KNDF da irin aiyukan da ta sanya a gaba na ci gaban al’uma da kuma hanyoyin samar da abubuwan kyautata rayuwar al’umar yankin domin ganin  an sami zamantakewa mai kyau.

A jawabinsa na maraba, shugaban kungiyar kuma daya daga cikin mutane masu kishin yankin da suka assasa kungiyar, Alhaji (Dokta) Wada Waziri Ibrahim, Sa’in Kano kuma hakimin Makoda ya fayyace dukkanin manufofin kungiyar, sannan ya sanar da dalilai da suka sanya aka yi tunanin kafa kungiyar da kuma irin aikace-aikacen da zasu tinkara domin ciyar da kano ta arewa gaba.

Sannan ya bayyana cewa kowa yana da muhimmancin gaske a wannan kungiya dkn haka yayi jan hankaki da kira ga daukacin mutanen shiyyar arewacin kano mai kananan hukumomi 13, dasu tsaya sosai wajen ganin sun bada gagarumar gudummawa wajen bunkasa yankin ta kowane fanni, inda kuma yayi fatan alheri ga dukkanin mutanen da suka halarci bikin kadfamar da kungiyar ta KNDF.

Da yake kaddamar da kungiyar, gwamnan kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin kwamishinan ma’aikatar ruwa ta jihar kano,  Alhaji Usman Sule Riruwai yace ko shakka babu abinda mutanen kano ta arewa suka yi na kafa wannan kungiya yayi daidai, sannan ya jaddada cewa gwamnatin jihar ta kano tana alfahari da yaffa al’uma suka fara tunanin tashi tsaye wajen nemawa yankunan su mafita a kungiyance.

Sannan ya bukaci dukkanin al’umar kano ta arewa dasu baiwa wannan kungiya hadin kai da goyon baya ta yadda zata cimma nasarori masu yawa vikin aiyukanta, tareda jinjinawa Hakimin Makoda kuma Sa’in kano Dokta Wada Waziri bisa gagarumar gudummawar da ya bayar har aka kawo lokacin kadfamar da kungiyar.

Daga karshe an kaddamar da kalandar kungiyar ta KNDF  kuma aka tara kudi fiye da naira miliyan guda inda gudummawa mafi tsoka ta   naira  dubu 500 fita daga hannun wakilin kano ta arewa a majalisar dattawa ta kasa watau Sanata Barau I. Jibrin,  ta hannun hadimin sa, Alhaji Shitu Madaki Kunchi,  inda  kuma jami’in hulda da jama’a na kungiyar kuma wakilin gidan radiyo kano na gidan gwamnati Alhaji Habibu Liman ya jaddada cewa kungiyar zata ci gaba da bayyana aikace-aikacen ta ta yadda kowa zai fahimci manufar ta da kuma kyawawan tanade-tanaden ta na alheei ga al’uma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.