AN ZABI SABON SHUGABAN KUNGIYAR MASU SHAYI TA JIHAR FILATO  

0
74

 Isah  Ahmed, Jos

‘YAN kungiyar masu shayi ta kasa reshen jihar Filato, sun zabi Malam Abubakar Ibrahim Madaki Mangu a matsayin sabon shugaban kungiyar. ‘Yan kungiyar masu shayin sun zabi sabon shugaban nasu ne, a karshen makon da ya gabata a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

Da yake jawabi bayan kammala zaben shugaban kungiyar masu shayi ta Najeriya Alhaji Shu’aibu Abubakar ya bayyana matukar farin cikinsa, kan yadda aka gudanar da zaben lafiya.Ya ce wannan zabe da suka gudanar ya zo masu da  sauki sosai,  domin an sami sulhu  tsakanin ‘yan takarar.

Ya yi kira ga sabon shugaban ya  rike wannan  amana da adalci musamman ganin yadda ‘yan wannan kungiya suka taru suka zabe shi a matsayin shugaban wannan kungiya.

Har’ila yau ya yi kira ga sabon shugaban  ya  tashi tsaye wajen ganin ya kwatowa ‘yan  kungiyar hakkokinsu, a wajen hukumomi da kamfanonin da suke sarrafa kayayyakin shayi.

Hakazalika ya yi kira ga ‘yan  kungiyar  su baiwa sabon shugaban   goyan baya da hadin kai domin ya sami nasarar ayyukan dake gabansa.

Daga nan ya yi kira ga ‘yan  kungiyar  su rike wannan sana’a tasu  da daraja domin  sana’a ce mai matukkar mahimmanci a duniya.

A nasa jawabin sabon shugaban kungiyar masu shayin  ta jihar Filato  Malam Abubakar Ibrahim Madaki Mangu ya bayyana cewa gaskiya ya yi matukar farin ciki da wannan zabe da aka yi masa.

Ya bada tabbacin cewa zai yi iyakar kokarinsa  wajen ganin an bi dokoki da tsarin wannan kungiya a kan wannan matsayi da aka zabe shi.

Ya ce asalin kafa wannan kungiya shi ne masu shayi su  taimaki junansu, don haka ya ce  zasu yi iyakar kokarinsu wajen ganin sun taimaki junansu.

Ya yi kira ga dukkan ‘yayan wannan kungiya su basu goyan baya da hadin kai don ganin sun sami nasarar kudurorin da suka sanya a gaba.

Wakilan ‘yan kungiyar da suka gudanar da wannan zabe, sun fito ne daga kananan hukumomin  Kanke da Panshing da Kanam da Bokkos da Mangu da Barikin Ladi da Bassa da Jos ta arewa da kuma Jos ta gabas, dake jihar ta Filato.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.