KARANCIN TUMATUR NE YA KAWO TSADARSA-AMINU YAHAYA  

0
47

Isah  Ahmed, Jos

SHUGABAN kasuwar ‘yan tumatur dake farar gada a garin Jos babban birnin jihar Filato, Alhaji Aminu Yahaya Inusa ya bayyana cewa karancin tumatur ne da ake fuskanta a bana ya kawo tsadarsa. Alhaji Aminu Yahaya Inusa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, a garin Jos babban birnin jihar Filato.

Ya ce kamar a nan jihar Filato  bana manoman tumaturi  a jihar,  sun noma tumatur  amma Allah yasa an sami matsalolin kankara da wasu cututtuka da suka kashe tumaturin. Ya ce wannan ne yasa tumaturin  bai wadata ba har ya zuwa wannan lokaci da ake ciki, don haka aka sami  karincinsa shi  ne yasa yake tsada.

Ya ce kamar abin da ya shafi jihohin  Gombe da Kano da Kaduna can ma an sami irin wannan matsala,  don haka  yanzu tumaturin yake  tsada a ko’ina.

Alhaji Aminu Yahaya ya yi bayanin cewa a gaskiya an rungumi  harkokin kasuwancin  sayar da tumaturi  a kasar nan. Domin a kananan harkokin kasuwanci, babu wanda zaka yi yanzu yanzu ka sami abin da zaka ci kamar kasuwancin tumaturi.  Ya ce don haka yanzu da matan aure da zawarawa da sauran matasa  suka rungumi wannan harkokin kasuwanci na sayar da tumaturi.

Ya yi kira ga  gwamnati ta rika baiwa bangaraen noma kaso mafi tsoka a kasafin kudin Najeriya, domin  yanzu manoma ne suke rike da Najeriya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.