Kungiyar BMO Ta Bukaci A Cire Sunan Matthew Kukah Daga Cikin Kwamitin Sulhu Na Kasa

0
36

Daga Usman Nasidi

KUNGIYAR masu kare rajin Buhari a kafar sadarwa ta zamani (BMO) sun bukaci shugaban kasar da ya cire sunan Shugaban darikar Katolika na jihar Sokoto, Matthew Kuka, daga cikin kwamitin zaman lafiya na kasa, wanda tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar ke jagoranta.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne a ranar Laraba, cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugabanta, Niyi Akinsiju, da kuma sakatarenta, Cassidy Madueke, a Abuja.

Kungiyar ta ce bayyana bukatar cire sunan Mr. Kuka ya zama wajibi a garesu duba da cewa, shi (Mr. Kuka) ya bayyana soyayyarsa da goyon bayansa a fili ga dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Sai dai a baya bayan nan Mista Kukah ya bayyana dalilinsa na zuwa zaman sulhun Atiku da Obasanjo, yana mai bayyana cewa hakan da yayi ba wai siyasa bane, illa dai zama ne na sulhu tsakanin mutanen da ke gaba da junansu.

Kungiyar, a cikin sanarwar, ta ce “Mun yi matukar mamaki, kamar yadda muka san cewa kowanne dan Nigeria ma na cike da mamaki a wannan rana, ganin Bishop Kukah a cikin tawagar abokan hamayya, da sunan yaje sulhu tsakanin Atiku da Obasanjo”.

Kungiyar BMO ta kuma yi ikirarin cewa bayanan Mr Kuka na baya bayan nan da ya ke ikirarin cewa shine ya shirya wannan sasantawar, hakan ya nuna cewa yaje sulhun ne don a hada kai tsakanin bangarorin biyu a yaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Ba haka aka san shuwagabannin addinai ba, musamman shi da ake kallo a matsayin wata fitila a cikin kwamitin wanzar da zaman lafiya na kasa. Amma a yanzu ya nuna bangaranci, kuma hakan ba mai karbuwa bane a garemu”

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.