Shehu Sani Ya Mika Ta’aziyyar Sa Na Bajimin Malamin Da Ya Rasu A Kaduna

0
45

Daga Usman Nasidi

FITATCEN Sanatan nan wanda ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa watau Sanata Shehu Sani yayi magana game da ficewar sa daga Jam’iyyar APC mai mulki a kurarren lokaci bayan ana sa ran zai yi takara a 2019.

Sanatan na Yankin Tsakiyar Jihar Kaduna bai yi rububin tserewa daga Jam’iyyar APC a lokacin da manyan ‘Yan siyasa su ke sauya-sheka zuwa PDP. Sanatan yace ya zabi ya bar Jam’iyya APC ne a lokacin da ya ga dama.

‘Dan Majalisar yayi wannan jawabi ne a kaikaice a shafin sa na sadarwa na Tuwita bayan ya sanar da cewa ya bar Jam’iyyar ta APC.

Bayan nan dai Sanatan yayi jimamin rashin wani babban Shehi wanda ya rasu kwanan nan a Kaduna.

A makon nan ne babban Limamin da ke sallah a Masallacin Yahaya Road watau Imam Hassan Muhammad ya cika. Sanatan ya mika ta’aziyyar sa ga Iyalin Marigayin inda yayi addu’a Ubangiji ya saka masa da gida a Aljannah.

Bayan nan kuma Sanatan yayi tir da hare-haren da ‘Yan Boko Haram su ka kai a Jihar Borno sannan kuma yayi Allah-wadai da rikicin da ake yi a cikin Garin Kaduna yana mai neman a zauna lafiya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.