A  Bullo Da Shirye-Shirye Domin Kara Tallafawa Manoman Najeriya – Farouk AFAN

0
39

JABIRU A HASSAN,  Daga Kano.

SHUGABAN kungiyar manoma ta kasa watau AFAN reshen jihar kano, Alhaji Farouk Rabiu Mudi yayi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi dasu kara bullo da tsare-tsare na tallafawa manoman kasarnan domin ganin an cimma manufofin gwamnatin tarayya na  wadata kasa da abinci.

Yayi wannan kira ne a zantawarsu  da wakilin mu a ofishin sa, tareda jaddada cewa manoman kasarnan suna kokari sosai wajen samarda kaso mai tsoka na dukkanin nau’in kayan amfanin gonar da ake samar wa a sassa daban-daban dake fadin kasar nan duk da irin kalubalen da suke fuskanta na bukatar tallafi.

Alhaji Farouk Rabiu ya sanar da cewa idan aka kara samarda hanyoyi na taimakon manoma, ko shakka babu kwalliya zata biya kudin sabulu ta fuskar noma musamman ganin yadda wannan gwamnati take kokarin kawo sauyi a tsarin aikin gona a kasarnan.

Bugu da kari shugaba Farouk Rabiu ya nunar da cewa Najeriya tana da kasar noma mai yalwa da dausayi, idan aka kara samar da yanayi mai kyau ga manoma  za’a  sami ingantuwar al’amura ta fannin noma da samar da aiyukan yi ga miliyoyin al’uma rani da damina.

Dangane da bikin baje kolin kayan amfanin gona da aka yi a kano kuwa, Alhaji Farouk Rabiu Mudi ya nuna gamsuwar kungiyar AFAN reshen jihar kano bisa yadda manoma da kamfanonin samar da kayan aikin gona da kuma masu  sarrafa kayan amfanin gona suka baje kayayyakin su kuma manoma suka sami karin ilimi kan  ssbbin dabarun noma.

A karshe,  shugaban kungiyar ta AFAN yayi amfani da wannan dama wajen yin godiya ta musamman ga gwamnatin jihar kano saboda kokarin da take yi na bunkasa noma da kiwo batare da nuna kasala ba, sannan yayi fatan alheri ga  kwamishinan gona Dokta Nasiru Gawuna bisa nadin sa da akayi a matsayin mataimakin geamnan jihar ta kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.