YADDA ABOKAN ANGO MUTUM 7 SUKA RASA RAYUKANSU A HADARIN MOTA

0
69

 Isah  Ahmed Daga Jos

AL’UMMAR garin Bokkos da ke cikin Jihar Filato  sun shiga cikin tashin hankali da dumaucewa, bayan da suka sami labarin wani mummunan hadarin mota, da ya yi sanadin rasuwar wasu matasan garin, mutum 7  a ranar asabar din da ta gabata.

 Su dai wadannan matasa, da suka rasa rayukansu Amadu Haruna da Sham’unu Ibarahim da Bashir da Hassan Tahir da Haruna Musa da Idris Rabi’u da kuma Abubakar Adam. Sun gamu da wannan hadari ne a kusa da garin Toro, da ke jihar Bauchi a  lokacin  da suka dawo daga daurin auren abokinsu, mai suna    Aminu Garba da amaryarsa Zainab Abdullahi da aka daura a garin Magama Gumau, a wannan rana.

 Da yake yiwa wakilinmu karin bayani kan yadda  al’amari ya faru, wani dan uwan wadannan matasa da ya halarci wajen  daurin auren Alhaji Adamu Muhammad [Chabori]  ya bayyana cewa abin da ya faru shi ne sun taso daga  garin Bokkos  da ke jihar Filato, don su  je daurin aure a garin Magama Gumau da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi a ranar asabar din.

 Ya ce “bayan sun je an daura auren,  sun zauna sun ci abinci. Sai suka  cewa wadannan abokan ango da  hadari ya rutsa da su,   su yi gaba suna zuwa, domin su  zasu taho da  amarya.”  

Alhaji Adamu Muhammad [Chabori]  ya yi bayanin cewa wajen karfe daya na rana, sai aka kira su a waya,  aka ce masu ‘yan uwansu sun yi hadari a hanya. Ya ce  nan take sai suka taso domin su zo su ga abin da ya faru. Ya ce suna zuwa kusa da asibitin Toro, a wata  gangara  sai suka  sami motar wadannan angwaye, kirar Sharon  ta kauce hanya, ta fada cikin wani rami. Ya ce ana kyautata zaton motar, ta kauce  hanya ne  saboda da gudun da direban yake yi.

Ya ce mutane 8 ne a cikin wannan mota, kuma mutane 7 ne suka rasu, direban ne kawai ya tsira da ransa, yana kwance a asibiti.

 ‘’Da muka zo aka fito da su, aka kawo wata babbar mota aka debe su, a lokacin da aka fito da su mutane 3 sun riga sun rasu,  a asibitin Toro ne  mutane 3 suka rasu, mutum 1 kuma ya rasu a asibitin Plateau hospital  da ke garin Jos. Daga nan muka kwashi gawarwakinsu muka tafi da su zuwa garin Bokkos muka yi masu jana’iza a yammacin wannan rana’’.

Ya ce dukkan wadannan  matasa  ‘yan kasa da shekaru 30 ne,  kuma mutum 2 ne kawai   suka yi aure.

Ya ce a gaskiya wannan abu da ya faru, ya sanya sun  dimauce  a wannan gari,  maza da mata da iyaye gabaki daya musulmi da kirista,  saboda mutuwar wadannan matasa.  Kuma  da kiristocin wannan gari ‘yan kasa da yarwabawa da yamurai,  aka je aka yi jana’izar wadannan matasa.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari angon da aka daurawa auren, Aminu Garba  ya bayyana cewa  ya yi matukar kaduwa da faruwar wannan hadari. Ya ce don  haka duk da yana wajen  daurin auren, amma bai iya zuwa wajen da wannan hadari ya faru ba.

Ya ce  wadannan matasa da wannan al’amari ya rutsa da su, abokansa ne  kuma suna tare  a kowanne lokaci.

Shima da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari sakataren Kungiyar matasa Karamar Hukumar Bokkos  Kwamaren Mabur Tokshik  ya bayyana cewa  gaskiya wannan abu da ya faru, wani babban abin bakin ciki ne ga al’ummar  yankin gabaki daya.

Ya ce domin wadannan matasa da hadarin nan   ya rutsa da su, matasa ne da ake tunanin nan gaba zasu iya zuwa su bada gudunmawa, wajen cigaban yankin da kasa gabaki daya.

Ya ce don haka a matsayinsu na shugabannin matasan  yankin, suka fito gabaki dayansu suka nuna juyayi kan wannan rashi da suka yi.  Kuma suka tsaya wajen ganin an  yi jana’izar wadannan matasa, batare da nuna  banbancin addini ko kabila ba, domin suna zaune lafiya da junansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.