DA YARDAR ALLAH ZAN KAWO ZAMAN LAFIYA A FILATO-MARGARET INUSA

0
21

Isah Ahmed Daga Jos

 MARGARET Inusa ita ce  ‘yar takarar kujerar gwamnan Jihar Filato karkashin jam’iyyar ADP, a zabe mai zuwa na shekara ta 2019. A wannan tattaunawa da tayi da wakilinmu, ta bayyana cewa tun da maza sun gaza wajen samar da zaman lafiya, a Jihar Filato. Idan aka zabe ta gwamnan Jihar Filato a zabe mai zuwa, da yardar Allah zata kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar.

 Ga yadda tattaunawar ta kasance

 GTK: Da farko zamu so muji tarihin rayuwarki.

Margaret Inusa: To ni dai sunana Margaret Inusa, kuma  an haife ni ne a  garin Jos, a watan Yuni na shekara ta 1975. Kuma iyayena sun fito ne daga Karamar Hukumar Panshing da ke wannan Jiha ta Filato. Nayi karatu a nan Jos, kuma ina da ‘yaya biyu. Ina ayyukan Kungiyoyi tare da gabatar da shirye shirye a  Rediyo.

A yanzu  kuma  ni ce ‘yar takarar kujerar gwamnan Jihar Filato,  karkashin jam’iyyar ADP. Bayan da aka  yi zaben fadda gwani na takarar  kujerar gwamnan Jihar Filato, a wannan jam’iyya. Allah ya sharewa  mata da matasa da sauran al’ummar Jihar Filato hawaye, aka amince aka tsayar da ni takara  a karkashin wannan jam’iyya. Bayan janyewar da sauran ‘yan takara mutum uku suka yi.

GTK: Ma ye ya karfafa maki gwiwar fitowa wannan takara?

Margaret Inusa: A duk lokacin da ‘yan jaridu da sauran jama’a    suka yi mani irin wannan tambaya, abin da nake fada masu shi ne, ni ba ‘yan siyasa bace, ni mai kishin kasa ce.

Kuma   ganin irin abubuwan da suke faruwa a wannan Jiha, yasa naga bai kamata mu rungume hanu muna kallo  mu barwa  ‘yan siyasa   abubuwa suna  cigaba da lalacewa ba.

Kamar yadda na fada ni ba ‘yar siyasa bace, ni mai kishin kasa ce. Amma abubuwan da suke faruwa a Jihar nan, na rashin zaman lafiya shi ne ya karfafa mani gwiwar fitowa wannan takara.

Domin a wannan Jihar aka haifeni kuma a wannan Jiha na girma. Akwai lokacin da muke makarantar sakandire a wannan gari na Jos, na tuna lokacin da zamu tashi a kafa. Mu bi lungu mu shiga unguwar Rogo muje mu fita ta farar gada, mu tafi Zariya Road. Amma yanzu haka ba zata iya yuwa ba, domin an riga an shuka mana rashin kaunar juna a zuciyarmu.

Ni a ra’ayina, bana son na duba wannan matsala a bangaren siyasa. ina son na duba wannan matsala  a matsayina na mai kishin kasa.

A matsayina na uwa ina son na hada kan al’ummar Jihar Filato ‘yan kasa da sauran mazauna Jihar,  kirista da musulmi da ma wadanda basu da addini mu hada kai, mu zauna lafiya  domin cigaban wannan Jiha.

Muna maganar bunkasar Jihar nan. Allah ya albarkaci Jihar nan da abubuwa da dama. Idan ka dubi bangaren aikin noma da bangaren wuraren yawon bude ido da bangaren harkokin ma’adanai  Allah ya albarkaci  Jihar nan, da wadannan abubuwa.

A kullum muna kiran masu zuba Jari na waje, kan  su zo su zuba Jari a Jihar nan. Babu wanda zai zo daga waje ya zuba Jari a Jihar nan, idan babu zaman lafiya.

Don haka babban abin da zan sanya a gaba idan aka zabe ni, shi ne maganar  samar da zaman lafiya da yafewa juna kan abubuwan da suka faru a baya.

Idan Allah ya bani wannan kujera zan  kira kowa da kowa da wanda aka kashe  dan’uwa da wanda ada yana da harkokin kasuwanci aka lalata. Mu  zauna a biya wadanda suka rasa ‘yan uwansu da dukiyoyinsu diyya. Domin idan aka kashewa mutum dan uwa aka biya shi diyya, ko kuma aka kona maka dukiya ko wurin harkokin kasuwanci  aka biya ka diyya, ka koma ka cigaba da harkokinka za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Don haka zaman lafiya da yafewa juna shi ne babban abin da zan sanya a gaba. Domin ina son zaman lafiya. Ina son a kowa ya girmama mabiya addinan da yake tare da su. Domin ya kamata mu girmama juna mu zauna lafiya, domin Jihar nan ta cigaba. Idan ka shiga unguwar Rogo da Bauchi road da unguwar Apata da Rikkos da ke nan garin Jos, duk zaka ga babu hanyoyi masu kyau.

An ce za a tallafawa mata da  matasa amma gashi shekaru 4 har sun kare, bamu ga abin da aka yi ba.

Don haka ya kamata al’ummar Filato, su gane cewa ni uwa ce, idan uwa ta debi ‘yayanta ta hada su wuri daya za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali. Domin babu macen zata so taga ‘yayan ta suna gaba da juna. Saboda haka ina son inzo ba a cikin siyasa ba,  a matsayin mai kishin Jihar Filato, domin na ga Jihar ta  cigaba.

GTK: Ganin tun da aka dawo mulkin siyasa a Kasar nan, an yi gwamnoni maza da dama a Jihar nan,  amma har yanzu ba a sami zaman lafiya ba, kina ganin a matsayinki na mace zaki iya kawo zaman lafiya a Jihar nan, idan aka zabe ki?

Margaret Inusa: Ina son na tabbatar maka cewa mace ce ta san zafin mutuwa, domin  ita ce ta san wahalar da tayi wajen haihuwa. Ubangiji Allah ya bamu Jihar Filato. Wato Filato kamar da ne da aka haifa a wurina. Idan ka dubi sauran   Jihohin da ya kamata ace yanzu  mun fi su,  yanzu sun fi mu.

Don haka tun da maza sun yi, sun kasa wajen samar da zaman lafiya a Filato. Ina kira ga al’umma Jihar Filato su bani dama, domin a gwada mace a gani ko zata iya ko ba zata iya ba.

Ni ba zan shigo gwamnati wani ya kalleni ya ce don ni mace ce ba zan iya yin komai ba. Babu shakka mulkin Filato ya gagari maza, don haka  a baiwa mata dama.

GTK: Wato kina ganin idan aka zabe ki, zaki yi abin da yafi mazajen suka yi a gwamna a Jihar Filato?

Margaret Inusa: In Allah ya yarda zan yi abin da yafi na gwamnoni maza  a Jihar Filato musamman wajen samar da zaman lafiya. Ina da zuciyar yin haka, domin a ‘yan shekarun nan nawa, naga abubuwa da dama a duniya, nayi aiki da mutane iri  daban daban, naje kasashen waje naga abubuwa da dama, don haka babu abin da zai gagareni.

Saboda haka ina kira ga al’ummar Jihar Filato, su bani dama domin zan share hawayensu.

GTK: Ya ya kika ga yanayin yadda mata suka rungumi harkokin siyasa a kasar nan?

Margaret Inusa: A gaskiya kamar a wannan zabe da za a gudanar a shekara ta 2019, akwai dan cigaba dangane da shigar mata cikin harkokin siyasa, a kasar nan. Amma  duk da haka abin har yanzu mu mata  bai yi mana kyau ba. Domin kamar ni, tun da na fito takarar nan, naga abubuwa da idona.

Kudaden da ya kamata a dauka a baiwa mace don a  bata goyan baya, an ki. Idan aka yi magana sai ace ai mace ce babu abin da zata yi. Wannan yana kashewa mata gwiwa wajen fitowa takara a qasar nan.

Kuma idan ka dubi jam’iyyun kasar nan, basu taimakawa mata yadda ya kamata ba. Amma ni zan  godewa wannan jam’iyya ta ADP da nake takara karkashinta, domin sun bamu takardar tsayawa takara kyauta, batare da mun biya ko kwabo ba. Amma sauran jam’iyyu, sai dai kawai sun dan ragewa mata kudaden takardun tsayawa takarar ne kawai. Ya kamata a gane cewa mata karfinsu bai kai yadda zasu fito da kudade su zuba a cikin siyasa ba. Don haka ya kamata a qarfafawa mata gwiwa, a taimaka masu wajen shiga harkokin siyasa a Nijeriya.

GTK: Wanne kira ko sako ne kike da shi zuwa ga al’ummar Jihar Filato?

Margaret Inusa: Kira na ga al’ummar Jihar Filato shi ne idan lokacin zaben nan na shekara ta 2019 yazo, su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi mutane nagari, wadanda suka cancanta.  A wannan  karon ba jam’iyya za a zaba ba, za a zabi cancanta ne, domin yin haka ne zai kai mu ga nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.