El-Rufa’i Ya Taimakawa Harkokin Noma Sakamakon Kawo Kamfanin Olan-Abdul’azeez Gidan Dutse

0
16

 Isah Ahmed Daga  Jos

WANI babban manomi da ke zaune a kauyen Gidan dutse da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, Alhaji Abdul’azeez Yakubu Gidan dutse ya bayyana cewa gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i, ya taimakawa manoman Jihar Kaduna da sauran manoman da suke makotaka da Jihar.

Sakamakon kawo kamfanin sarrafa kayayyakin amfanin gona na Olan zuwa Jihar. Alhaji Abdul’azeez Gidan dutse ya bayyana haka ne,  lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce duk manomin da  da ya ce baya son gwamna El-Rufa’i bai yi daidai ba, domin ya kawo wa manoma kamfanin sarrafa amfanin gona na Olan a Kaduna.

Ya ce ada sai manoman Jihar Kaduna sun kai masarar da suka noma Fatakwal ko Legas ko yankin Iyamurai. Ya ce amma yanzu a Jihar Kaduna sakamakon zuwan wannan kamfani na Olan, manoman sukan kai masarar da suka noma  su   sayarwa wannan kamfani, batare da wata matsala ba.

Ya ce bayan haka El-Rufa’a ya gayyato babban dan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote zuwa Jihar Kaduna, a inda  ya sami fili zai yi kamfanin fulawa a Jihar.

Ya ce wannan ba karamin taimakawa manoman zai yi ba, domin duk kayayyakin amfanin gonar da manoma zasu noma, idan babu mai saye sun  yi aikin banza.

Alhaji Abdul’azeez ya yi bayanin cewa  ya fara  noman masara  tun a shekara ta 1982,  lokacin da tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya kawo  masara Najeriya. Ya ce shi  ne ya fara karbar noman masara, a yankin Karamar Hukumar Lere.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.