Wani Matashi ya yiwa Mahaifiya da Surukarsa Fyade a Jihar Kaduna

0
117

Daga Usman Nasidi

RAHOTANNI na bayyana cewar, hukumar ‘yan sanda ta Najeriya ta kai daduma kan wani Matashi dan shekara 32 a duniya, David Shakari, mazauni karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna dake Arewacin Najeriya.

Hukumar bisa jagorancin reshen na ta leken asiri ta samu nasarar cafke Shakari bisa mummunan laifin da ya aikata na yiwa Maifiya da Surukarsa fyade a garin na Kaduna.

A yayin da jami’an tsaro ke titsiyen wannan Matashin da ya nuna hali na ‘dan yau, Shakari ya zargi kasancewarsa cikin maye da nasabar wannan aika-aika da ya ke ci gaba da nadama a kanta.

Shakari wanda a halin yanzu na tsare a babban ofishin ‘yan sanda na Katari, ya amsa laifinsa na murkushe mahaifiyarsa ‘yar shekara 65 da kuma Surukarsa ‘yar shekara 70 cikin duhu na dare.

Rahotannin sun kara da cewar Shakari ya aikata wannan munanan laifuka a karo daban-daban cikin shekarar 2017 da ta gabata, da wannan dabi’a ta sanya Uwargidansa ta kauracewa zama tare da shi.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wani dan siyasa can kasar India, M. J Akbar, ya musanta zargin yiwa wata ‘yar jarida fyade da cewar sai da ya nemi amincewar ta kafin sauke kwazabarsa ta da namiji a kanta.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.