Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yiwa Sarkin Awe, Abubakar Umar Ii Rasuwa

0
87

Daga Usman Nasidi

HADIMIN gwamnan Umaru Al-Makura kan yada labarai, Mista Yakubu Lamai ne ya tabbatarwa manema labarai rasuwar a birnin Lafia.

Ya ce basaraken mai daraja ta daya ya rasu ne a safiyar yau Asabar a wani asibiti da ke Abuja.

Ya ce basaraken ya rasu bayan ya yi fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 69 a duniya bayan ya kwashe shekaru 33 a kan kujerar sarautar Awe.

A sakon ta’aziyarsa, gwamna Al-Makura ya bayyana cewar ya girgiza da jin labarain rasuwar sarkin wanda ya kasance mutum ne mai kaunar zaman lafiya da hada kan al’umma.

Ya yi kira da al’ummar jihar suyi amfani da rasuwar sarkin a matsayin dama da za su yiwa junansu afuwa kana su kara tabbatar da zaman lafiya a jihar.

An yi jana’izar sarkin kamar yadda koyarwar addinin islama ta tanada.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.