Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Kwashe Kwanaki Tana Gumurzu Da ‘Yan Shi”A   A Abuja 

0
46

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR sojan Nijeriya tatabbatar da  mutuwar   mabiya Shi’a uku sunce sun  mutu a wani mummunan artabu tsakaninsu na tsawon kwanaki a Abuja.

ko da yake mabiya Shia sun ce an kashe musu kusan mutum 50.

Hujjar da sojin suka kafa da bidiyon Mista Trump ta jawo musu mummunar suka daga bangarori da dama na al’uma.

Watakila hakan ne ya sa ranar Juma’a rundunar sojin ta goge sakon bidiyon ko da yake ba ta fadi dalilinta na daukar matakinba.

Gabanin goge bidiyon, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki sojojin  da kashe ‘yan Shi’a, inda kuma ta ce zanga-zangar ‘yan Shi’ar ta lumana ce.

Sai dai mai magana da yawun sojojin Burgediya Janar John Agim ya ce sun yi amfani da harsasai masu rai ne ga masu zanga-zanga saboda suna dauke da makamai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.