Gwamnatin Zamfara Ta Fara Cika Alkawari Game Da Bindigogi

0
45

Mustapha Imrana Abdullahi

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Fara Cika alkawarin da tayi game da batun wadanda aka kama suna dauke da Bindiga ba bisa ka’ida ba a duk fadin kananan hukumomin Jihar baki daya.

Kamar dai irin yadda Gwamnatin ta Yaya ta a kafafen yada labarai cewa dukkan mutumin da ya kawo ma Gwamnati wata bindigar da ake ajiye da ita ko aka kwato daga hannun wani ko wasu ba bisa ka’ida ba za a ba mutum kyautar Kudi naira miliyan daya.

Hakan ta faru inda a cikin satinnan Gwamnatin ta bayar da Kudi miliyan hudu ga wadansu bindigogi hudu da wasu mutane suka kawo mata.

Kwamishinan ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautun gargajiya na Jihar ne ya Mika kudin a madadin Jihar Zamfara.

An dai samu bindigu biyu ne daga wadansu mutanen da suka kamo masu dauke da su da karfin Tuwo, Sai kuma wani Direban da ya bi ta kan wadansu yan fanshi biyu da ya hayesu a kan hanyar zuwa Jibiya cikin Jihar Katsina daga Jihar Zamfara, kuma nan take aka bashi miliyan biyu ya kama gabansa.

Kwamishinan dai ya ce za a rika bayar da wannan kudin ne daga cikin irin kudin da ake kula da harkokin tsaro da su.

Su dai mutane biyu da aka kama da karfin Tuwo dukkan su suna hannun jami’an tsaro ana gudanar da binciken kuma bindigun ma suna hannun jami’an yan sandan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.