Isa Ashiru Ya Karyata Jita Jitar Yarjejeniya Da Kungiyoyin Addini

0
30

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

DAN takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin Jam’iyyar PDP Honarabul Isa Mohammad Ashiru Ya bayyana cewa hakika an ja hankalinsa a game da labarin da ake ta yadawa kan wai ya kulla Yarjejeniya da wadansu Kungiyoyin addini domin zaben shekara 2019 Mai zuwa.

Kamar yadda ake yada jita Jitar akwai kamanceceniyar wai zai biya Ko sakamawa duk kan Kungiyoyin da ake maganar a Kansu idan sun taimaka Masa.

A don haka ne Honarabul Isa Mohammad Ashiru yake fayyace  komai domin a fahimta cewa Bai taba yin wata Yarjejeniya da kowa cewa idan ya taimake shi zai biya shi ba, babu wata kungiya Ko dai daikun mutane a duk fadin Jihar Kaduna.

Kasancewar akwai masaniyar cewa wadannan Kungiyoyin na addini ne Dan takarar karkashin PDP na nesan ta kansa da yunkurin irin wannan da yan dakon yada jita jita suke yi suna danganta lamarin da siyasa

“Ina kira da babbar murya kan cewa jama’ar Jihar kaduna suyi watsi da irin wannan jita Jitar da ake  yadawa, abin da ya bayyana da cewa yarfen siyasa ne kawai da wasu da suka karaya suke Jin tsoron kasancewarsa dan takarar Gwamna karkashin PDP a Jihar kaduna.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su bude idanunsu domin hakan zai sa su fahimci irin wadannan masu kokarin yi wa tafiyarsa kafar Angulu ta hanyar hada siyasa da batutuwa na addini domin haifar da bambancin Rikicin addini na din din din.

Duk bayanin nan na kunshe ne cikin wata takardar da kwamitin yada labarai na yakin neman zaben Isa Mohammad Ashiru (HIMACO) ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Ya ci gaba da cewa a matsayinsa na Dan takarar PDP zai ci gaba da fallasa duk kan wani Ko wasu yan koren da suke kwangilar kawo hargitsi Ko Nuna bambanci domin kawai hadamar darewa kan kujerar Mulki a don haka ne ya Shawarci jama’a da su shigo cikin jirgin tsira daga hannun yan Ko in kula da sunan shugaban ci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.