GWAMNA EL-RUFAI YA MAKA JAMI’AR ABU DA KADPOLY GABAN KOTU

0
104

Daga Usman Nasidi

GWAMNAN jahar Kaduna ya shigar da karar jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria ta jahar Kaduna, tare da kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya dake garin Kaduna, KADPOLY bisa kin biyan harajin kudi da suka kai naira biliyan tara da miliyan hamsin a jimlace.

gwamnan ya shigar da karar ne gaban kotun sauraron kararraki akan haraji, wanda ministan kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta kaddamar da shi, inda hukumar tattara kudaden haraji ta jahar Kaduna ke wakiltar jahar.

Da suke tsatstsage bayani a gaban kotun, hukumar tattara haraji ta jahar Kaduna ta bayyana cewa jami’ar Ahmadu Bello ta ki biyanta harajin naira biliyan shida da miliyan goma sha shida na ma’aikatanta, kudaden sun taru ne daga shekarar 2007 zuwa 2012.

Hak zalika shugaban kotun, Malam Umaru Adamu ya saurari karar da hukumar ta shugar da kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya dake garin Kaduna, KADPOLY, inda itama take zarginta da kin biyan harajin naira biliyan uku da miliyan uku daga shekarar 2007 zuwa 2012.

Ita ma gwamnatin jahar Kano ba’a barta a bay aba, inda a ranar Alhamis ta shigar da karar asibitin kasha ta gwamnatin tarayya dake Kano akan zarginta da rashin biyan harajin naira miliyan goma sha takwas da dubu dari shida.

Don haka gwamnatin jahar Kano ta hannun hukumar tattara mata kudaden shiga ta nemi kotu ta bayyana mata ko tana da damar kwatar kudaden daga hukumar asibitin ko kuwa.

Bugu da kari gwamnatin jahar Kano ta shigar da karar jami’ar Bayero ta Kano tare da ministan ilimi Adamu Adamu kan zargin jami’ar da rashin biyan harajin naira biliyan daya da miliyan tamanin da biyu tun data shekarar 2004 zuwa 2009.

Zuwa yanzu dai ana tsumayin hukuncin da wannan kotu da ministan kudi shamsun Ahmad ta kafa a ranar 5 ga watan Nuwamba don sauraron koke koken haraji, za ta yanke game da kararrakin da aka shigar gabanta.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.