Gwamna Lalong Mutum Mai Son Zaman Lafiya Ne – Inji Yahaya Kega 

0
64

 Isah Ahmed Daga Jos

WANI Jigo a jam’iyyar APC reshen Jihar Filato, kuma shugaban Kungiyar Dillalan mota ta kasa reshen Jihar ta Filato Alhaji Yahaya Muhammad Kega, ya bayyana cewa gwamnan Jihar Filato Simon Lalong mutum ne mai son zaman lafiya. Alhaji Yahaya Muhammad Yahaya Kega ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Ya ce a matsayinsa  na dan Jihar Filato kuma hausa Fulani gaskiya gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya cancanci a sake zabarsa karo na biyu, a matsayin gwamnan Jihar Filato.

Ya ce  matukar ba a sake zabensa ba, za a mayar da hanun agogo baya a Jihar. Domin  Lalong mutum ne mai son zaman lafiya. Baya cikin masu cin mutumcin jama’ar Jihar,  Kuma baya cikin wadanda suke karfafa ayi tashin hankali a Jihar.

Ya ce ya rungumi kowa da kowa a gwamnatinsa, babu ruwansa da maganar yare ko addini. Don haka ya cancanci al’ummar Filato musulmi da kirista da wadanda basu da addini su suke zabarsa. 

‘’Idan babu zaman lafiya babu abin da zai cigaba. A manta da wani batun gine gine, idan har za a zauna lafiya mai kasuwa ya tafi kasuwa yara su tafi makaranta sai a gode Allah. An sami daya daga cikin abubuwan cigaba. Dukkan sauran abubuwa ana dorawa ne kan zaman lafiya’’.

Ya ce gwamna Lalong ya yi kokari wajen biyan albashin ma’aikata Jihar, domin ba a binsa bashin ko kwabo na albashin ma’aikata a Jihar. Amma wasu gwamnonin duk da tallafin da shugaban kasa ya basu, sun kasa biyan ma’aikatansu albashi.  

Ya yi  kira ga al’ummar Filato su fito su nuna su mutane ne masu son zaman lafiya ne su sake zaben  gwamna Lalong domin shi mai son zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.