Karamar Hukumar Lere Ta Kaddamar Da Raba Kyautar Litattafai Ga Dalibai

0
30

 Isah Ahmed Daga Jos

SHUGABAN Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Alhaji Abubakar Buba, ya kaddamar da shirin raba kyautar litattafan karatu da rubutu ga dukkan daliban Makarantun Firamare na yankin, a Makarantar Firamare ta kauyen Bundu Kahugu da ke yankin.

Da yake jawabi lokacin da yake kaddamar da shirin, shugaban Karamar Hukumar Alhaji Abubakar Buba ya bayyana cewa  ya zabi ya kaddamar da raba wadannan litattafai ne, a  makarantar da take kauye domin ya ganewa idonsa irin matsalolin da suke damun makarantun Firamare na kauyukan yankin domin  magance su.

Ya ce  cikin  wadannan litattafai da za a rabawa daliban, baya ga litattafan rubutu, akwai  litattafan    koyon turanci da lissafi da kimiyya da takardun shedar rubuta sakamakon jarrabawa da kuma Satifiket na kammala Firamare.

‘’Daga yanzu a Karamar Hukumar  kada wani uba ya kara bayar da kudi don a baiwa yaronsa Satifiket na kammala Makarantar Firamare. Domin takardun satifikef  Tastimoniyal da muka kawo za ayi shekaru 5 basu kare ba a  Karamar Hukumar. Don haka yanzu Tastimoniyal da satifiket na kammala makarantar firamare a Karamar Hukumar Lere ya zama kyauta’’.

Ya yi  kira ga daliban  suyi amfani da litattafan  kamar yadda ya kamata. Domin an kawo su  ne don  inganta karatun Makarantun Firamare a Karamar Hukumar.

Har’ila yau ya yi kira ga iyaye su taimaka wajen kula da wadannan litattafai da za a rabawa ‘yayansu, kada su bari  su rika yaga wadannan litattafai.

Haka kuma ya yi kira ga malamai su  karantar da daliban Makarantun Firamaren, domin Karamar Hukumar  ba zata lamunci wani malamai ya rika  wasa da aikinsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.