Kasuwar Kara Ta Tulu Ta Kai Shekaru 100 Da Kafuwa- Haruna Mamuda

0
29

Isah Ahmed Daga Jos

SARKIN kasuwar kara ta Tulu da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Haruna Mamuda Tulu ya bayyana cewa wannan kasuwa ta kai sama da shekaru 100 da kafuwa.

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a kasuwar.

Ya ce tun da aka kafa wannan kasuwa ake kawo shanu. Yanzu  a kalla wannan kasuwa ta kai shekaru 100 da kafawa, kuma  kakanninsu ne tushen kafa wannan kasuwa.

Ya ce abin da yasa aka kafa wannan kasuwa suna kusa da dajin da ya taso tun daga Falgore da ke jihar Kano ya shigo dajin  Lame Bira da ke kusa da wannan yanki. Ya wuce har zuwa jihar Yobe,  kuma wannan daji baya rabuwa da Fulani.

Alhaji Haruna Mamuda ya yi bayanin cewa kamar shekaru biyu da suka gabata, sun sami matsalar rashin tsaro a wannan yanki, ta yadda varayi suka rika damunsu amma yanzu sun gode Allah domin sun sami tsaro. Don haka yanzu Fulani suna nan a gefan wannan yanki, ko ta ko’ina suna zuwa wannan kasuwa.

Ya ce ana kawo shanu wannan kasuwa a kowanne lokaci kuma  suna samun masu kawo shanu daga Ningi da ke Jihar Bauchi  da jihar Kaduna bayan wadanda ake kawowa daga wannan  daji. Kuma a takaice  kowace ranar kasuwa ana kawo shanu sama da 100.

Ya ce suna samun ‘yan kasuwa baki da suke zuwa sayen shanu  daga wurare daban daban kamar yankin Kaduna da Kano da Abuja da Jos da sauran wurare suna zuwa wannan kasuwa.

Ya ce babbar matsalarsu  ita ce Karamar Hukumar Toro bata yi masu  komai, na tallafi ba a  kasuwar.

‘’A yamma da jihar Bauchi babu kasuwar shanun da ta kai wannan kasuwa. Amma Karamar Hukumar Toro  bata yi mana komai ba. Sai dai su zo su karvi kudin shiga kawai su fita.Don haka muna rokon Karamar Hukumar Toro ta gina mana wannan kasuwa ta yi mana runfuna’’.

Ya ce babu shakka wannan kasuwa tana bada gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin yankin, domin dubban mutane suna cin abinci ta dalilin kasuwar kuma gwamnati tana karbar kudaden shiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.