Kungiyar Yakin Neman Zaben Buhari Zata Kafa Kwamitoci  A Dukkan Kananan Hukumomin Najeriya

0
38

 Isah Ahmed Daga Jos

GANIN yadda aka dage takunkumin yakin neman zabubbuka na shekara ta 2019. Kungiyar yakin neman zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta Buhari Compain Organisation [BCO] zata kafa kwamitocin wayar da kan jama’a kan irin ayyukan da Shugaban kasa ya yi a Kananan Hukumomin Najeriya da dukkan wuraren jefa kuri’a na kasar nan.

Shugaban Kungiyar Alhaji Danladi Garba Pasali ne ya bayyana haka, lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Ya ce zasu kafa kwamitoci a dukkan Kananan Hukumomin kasar nan 774,  da kowance rumfar zabe da ke Najeriya, don   wayar da kan jama’ar Najeriya kan irin ayyukan da shugaban kasa Buhari ya yi a Najeriya, a kusan shekaru 4 da ya yi kan kujerar shugabancin Najeriya.

Ya ce Shugaba Buhari ya yi faga da ‘yan ta’adda ya kawo zaman lafiya a kasar nan. Kuma  ya juya akalar ‘yan Najeriya zuwa ga harkokin noma. Yana aikin hanyoyin da aka manta da su a baya. Ya farfado da hanyoyin jiragen kasa.

Ya Kama wadanda suka sace kudaden kasar nan tare da kwato kudaden. Kuma ya  taimakawa masu kananan sana’o’i da  tsofaffi. Don haka ya ce  zasu   kafa wadannan kwamitoci, don su wayar da kan jama’a, kan wadannan ayyuka da shugaba Buhari ya yi.

Alhaji Danladi Pasali ya yi bayanin cewa ‘yan Najeriya ba zasu taba  mantawa da irin  illar da jam’iyyar  PDP ta yiwa Najeriya ba. Domin a shekaru 16 da suka  yi suna mulkin Najeriya, kowa yaga irin asarar rayukan da suka jawo  yi a Najeriya.

 ‘’A kalla a zamanin PDP an rasa rayukan ‘yan Najeriya sama da mutum miliyan 1, saboda  rashin imani. Don haka ‘yan Najeriya ba zasu yarda PDP ta kara dawowa mulkin  ba’’.

Ya yi kira ga talakawan Najeriya su kara daura damara su jawo hankalin ‘yan uwansu  wajen ganin shugab Buhari ya sake dawowa kan kujerar shugabancin kasar nan. Domin ya dora kasar nan kan tubalin gyara.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.