Ma Su Garkuwa Da Mutane Sun Sace Mataimakin Kwanturola Na Kwastam

0
88

Daga Usman Nasidi

AN kama wasu ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane su 7 bisa zarginsu da sace mataimakin kwanturola a hukumar kwastam, Justina Tanko, tare da kisan wani dan kasuwa, Chukwubuikem Ezenkwu.

Wadanda ake zargin su ne; Godspower Keenom, Zigabari Voonu, Oludofin Yakubu, Jastis Afangide, Dale Keliaga, Maxwell Barindom, da Tordi Barinaa. Rundunar babban sifeton rundunar ‘yan sanda ta martanin gaggawa ce bisa jagorancin Abba Kyari ta yi nasarar cafke mutanen a yankin Onne a jihar Ribas.

Rahotanni sun bayyana cewar ma su laifin sun karbi miliyan N5m kudin fansa kafin su saki jami’ar hukumar kwastam, Tanko.

Masu garkuwa da mutanen sun kashe dan kasuwar tare da jefa gawar sa a cikin wani tafkin ruwa duk da sun karbi miliyan N2.5m kudin fansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.