A Taimakawa Gajiyayyu Da Marayu A Wannan Wata – Dokta Isma’ila Abdullahi

0
219

 Isah Ahmed, Daga Jos.

WANI malamin addinin musulunci da Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa ta turo zuwa garin Jos, don gudanar da tafsirin Azumin watan Ramadan Dokta Isma’ila Abdullahi Musa, ya yi kira ga al’ummar musulmi da su dukufa wajen taimakawa gajiyayyu da marayu a wannan wata na Ramadan. Dokta Isma’ila Abdullahi Musa ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Ya ce ‘’muna kira ga jama’a da su taimakawa gajiyayyu da marayu domin taimakawa irin wadannan mutane a lokacin Azumin watan Ramadan,  zai iya sanya Allah ya sassauta mana halin da muke ciki na rikice rikice a kasar nan.  Saboda haka ina kira ga al’umma gabaki daya da su dage wajen ciyar da gajiyayyu da tallafawa marayu wajen ciyar da su da tufatar da su’’.

Har’ila yau, ya yi kira ga al’ummar musulman Najeriya da su tashi tsaye wajen yin addu’a ga wannan kasa dangane da miyagun abubuwan da suke faruwa na tashe tashen hankula a wasu sassan kasar nan, domin Allah ya kawo karshen wadannan tashe tashen hankula.

Haka kuma ya yi kira Jama’a d su rika nuna tausayi ga junansu suna taimakawa mara shi da marasa lafiya kuma su tsaya wajen aikata alheri a wannan wata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here