Ahmad Lawan Ya Lashe Zaben Zama Shugaban Majalisar Dattawa Na 9

0
240

Daga Usman Nasidi.

A Yanzu haka, Sanata Ahmad Lawan ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban majalisar dattawa na tara.
Sanata Ahmad Lawan ne a kan gaba yayinda ake ci gaba da kirga kuri’un zaben da aka gudanar na wanda zai jagoranci majalisar dattawa.

Lawan ya samu kuri’u 79 inda ya kayar da babban abokin adawarsa Sanata Ali Ndume wanda ya samu kuri’u 28.

An kammala zaben shugaban majalisar dattawa cikin kwanciyar hankali, a yanzu haka ana kan kirga kuri’un da sanatoci suka kada.

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole ma ya isa harabar majalisar dokokin.

Zuwa yanzu babu wani tsaiko da aka samu tun bayan fara kada kuri’a a zaben shugaban majalisar dattawa.

Sanatoci na kada kuri’a daya bayan daya sannan kuma suna ci gaba da zagayawa suna gaisawa da magana da juna cikin kwanciyar hankali.

‘Yar fargabar da aka taso da ita da farko ta kau.Rahotanni sun kawo cewa a yanzu haka an fara kada kuri’a a majalisar dattawa domin zabar wanda zai yi shugabancin majalisar ta tara.

An gabatar da tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar kujerar shugabacin majalisar.

A yanzu haka ana shirin fara zaben shugaban majalisar dattawa yayinda aka kira sanatoci domin su zo su kada kuri’a.
Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu haka ya nuna cewa rikici ya barke a majalisar dattawa yayinda ake shirin kaddamar da zabe.

Rikicin ya barke ne akan tsarin zaben da za a yi amfani dashi yayinda magatakardar majalisar ya karyata batun samun kowani umurni daga kotu wacce ta haramta amfani da tsarin zabe na sirri.

Zababbun yan majalisar dokokin kasar sun fara hallara a harabar majalisar ciki dogayen motocin bus.

Zababbun yan majalisar sun taso ne daga Transcorp Hilton Hotel. Da yawa daga cikinsu sun hallara tare da matayensu da misalin karfe 7:50 na safe.

Daya daga cikin manyan yan takarar kujerar shugabancin majalisar dattawa, Mohammed Ali Ndume, ya iso harabar majalisar dokokin gabannin rantsar da majalisar dokoki ta tara.

Ndume na kalubalantar tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar, Ahmad Lawan, wanda ya samu goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki.

Dan majalisar mai wakiltan Borno ta kudu ya isa majalisar da karfe 7:20 na safe sannan an gano shi yana ta musabaha da ma’aikatan majaliusar. Ndume ne zababben sanata na farko da ya fara hallara.

An tsaurara binciken tsaro sosai a kofofin majalisar dokokin tarayya daban-daban gabannin rantsar da majalisar dokoki ta tara wanda aka shirya gudanarwa a yau Talata, 11 ga watan Yuni, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Tun da misalin karfe 6:45 aka gano jami’an hukumar tsaro na sirri (DSS), jami’an yan sanda da kuma na Civin Defence a mashigin majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here