APC Na Fushi Da Gwamna Amosun Akan Jifan Da Aka Yiwa Buhari

0
66

Daga Usman Nasidi

JAM’IYYAR APC ta sha alkawarin daukar tsautsauran matakai akan wadanda suka dau nauyin hayaniya da hargitsin da ya faru a kamfen din jihar Ogun.

A shekaran jiya ne aka ga wasu bata gari suna jifan shugaba Buhari da leda da shirgi, lamari da ya sanya masu tsaronsa har hudu suka kare shi.

Sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar, Malam Lanre Issa-Onilu yace jam’iyyar tayi dana sanin harin da aka kaiwa shugaba Buhari da wasu jiga jigan jam’iyyar wanda ake zargin gwamna Ibikunle Amosun ne ya dau nauyi.

Issa-Onilu, yace hakan babban laifi ne kuma babu wanda yafi karfin dokokin jam’iyya don tilas ne bin su.

Mai magana da yawun jam’iyyar wanda ya shawarci mutane da kada su damu ko daga hankalin su akan abin ashshan da ya faru a ranar litinin din yace zasu cigaba da zagayen kamfen din kuma a fito kwai da kwarkwata don zaben yan jam’iyyar APC a zaben mai zuwa.

“Wannan wani nau’i ne na rashin da’a. APC kuma bazata lamunci hakan ba daga duk wani Dan jam’iyyar komai kuwa matsayin shi.

Jam’iyyar zata kara duba yanda aka ajiye zaune gari banza tare da shirya musu yanda zasu tozarta tare da kai hari ga shugaban kasa da kuma shuwagabannin jam’iyya. Jam’iyyar zata dau mataki ana kammala zabe.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here