Ba Mu Jidadin Sakamakon Taron Kungiyar Miyetti Allah Da Gwamnati Ba – Sale Bayari

0
427

Isah Ahmed, Daga Jos.

A WANNAN tattaunawar da shugaban Kungiyar ci gaban al’ummar Fulani ta Najeriya, ta Gan Allah Alhaji Sale Bayari da ya yi da wakilinmu, ya bayyana rashin gamsuwarsa, kan abubuwan da Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta kasa ta yi a tattaunawar ta da jami’an gwamnatin tarayya a wajen taron da suka gudanar a birnin Kebbi kwanakin baya kan matsalolin garkuwa da mutane da ake fama da shi a Najeriya da rikice rikicen Fulani makiyaya da manoma.

Har’ila yau ya kawo shawarar hanyoyin da gwamnati zata bi, ta kawo zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Najeriya.

Ga yadda tattaunawar ta kasance

GTK: A matsayinka na daya daga cikin jagororin al’ummar Fulani a Najeriya, maye zaka ce dangane da taron da kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah tayi da manyan jami’an tsaron gwamnatin tarayya a birnin Kebbi, kan matsalolin garkuwa da mutane da hare haren da ake kaiwa a kasar nan?

Bayari: To kamar yadda muka karanta labarin wannan taro a jaridu, da kuma muka ji al’ummarmu da suke wajen wannan taro da muka tura don su jiwo mana abubuwan da zasu faru a wajen taron.

A gaskiya, da mun dauka abubuwan da za ayi a wajen taron abubuwa ne na alheri amma daga baya da muka ji abubuwan da aka tattauna a wajen taron sai ya kasance a ra’ayina na shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Fulani ta Najeriya, ta Gan Allah ya zamo mani abin bakin ciki.

Domin mun ji cewa shugabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, sun je suna ciniki da gwamnatin tarayya, wai a basu kudi su zasu iya dakile ta’addancin da ake yi a cikin kasar nan, daga cikin al’ummar Fulani. Wannan abu ya bamu mamaki kwarai da gaske.

Kuma suka ce suna magana da yawun al’ummar Fulani ne gabaki daya, suka nuna cewa duk fashin da ake yi da sace sacen mutane da ake yi da kashe kashen da ake yi, tsakanin Fulani makiyaya da manoma, Fulani ne suke yi. Wannan babban bata sunan al’ummar Fulani makiyaya ne.

Da mun dauka za a je wajen wannan taro ne domin a tattauna, kan yadda za a yi a sami zaman lafiya kuma a nemawa bafulatani wajen da zai yi kiwo da burtali da zai tashi, idan ciyawa ta bushe ya fita yayi wani wuri kana a samar masa mashaya. Abubuwan da muka yi tsammani za a tattauna a wajen taron ke nan saboda wadannan abubuwa ne da za ayi amfani da su yau da gobe ta yadda ‘yaya da jikokinmu zasu amfana.

Amma ba wai ka dauki kudi ka baiwa mutum dan ta’adda mai kashe mutane da sace mutane tare da yin fashi. Kaje kace kana bashi kudi don ya daina wadannan abubuwa ba, idan ka bashi kudi kudin suka kare maye zai yi?.Saboda haka abin da muka sani shi ne, babu kudin da za a baiwa wadannan mutane da ba zasu kare ba. Saboda ba sana’a aka koya masu ba.

GTK; Wato a ganin ka wannan abu da aka yi a wajen wannan taro, an batawa al’ummar Fulani suna?

Bayari; An bata mana suna sosai wanda zamu dauki shekaru kafin mu gyara. Watakila sai mun dauki shekaru kamar 10 kafin mu gyara Ko kuma idan muka sami shugabanni masu kishi na kwarai wadanda suka san abin da suke yi.

GTK: To wadanne hanyoyi ne kake ganin gwamnati zata bi ta magance wannan matsala ta rikice rikice da garkuwa da mutane da ake zargin al’ummar Fulani?

Bayari: To ni dai gwamnatin nan tun farkon zuwan ta a shekara ta 2015, kafin a rantsar da shugaban kasa, akwai rahotan da na bata mai dauke da shafi 17, kan hanyoyin da za abi a zauna lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kasar nan. A lokacin naje na baiwa shugaban ma’aikatan shugaba Buhari na lokacin, wato shugaban hukumar kwastan na yanzu Kanar Hamidu Ali mai ritaya.

Bayan shekara daya na sake daukar wannan rahoto na kai masu, amma har yanzu shuru. Idan da sun aiwatar da kashi 15 cikin 100 na wannan rahoto, ina tabbatar maka da abubuwan nan basu baci haka ba.

Naje Jihar Zamfara a shekara ta 2013 lokacin da Janar Aliyu Gusau ya tura ni Jihar ya hada ni da gwamnan jihar, don gano abubuwan da suke kawo rikice rikice tsakanin Fulani makiyaya da manoma. Da gwamnatin Zamfara ta yi amfani da rahoton da na bayar a lokacin, da abin da zata kashe ba zai wuce naira miliyan 47 ba.

Saboda haka gwamnatin nan akwai shawarwari da muka bata, kan kananan hukumomi guda 105 na jihohi 21 na kasar nan, inda akwai matsala tsakanin Fulani makiyaya da manoma. Na fadi ga abubuwan da suke faruwa da idan ba a tare ba, ga abubuwan da zasu biyo baya. Ko sau daya ba a kira ni ba, ko ta waya ace an ga rahoto na an gode.

Don haka abin da ya kamata ayi a kasar nan shi ne ayi zama na fulani makiyaya da manoma, karkashin gwamnatin tarayya domin a tattauna yadda za ayi mahada a gayawa juna gaskiya kan yadda za a zauna lafiya kamar yadda ake zaune lafiya ada.

Mu abin da muke so gwamnati ta tabbatar tayi abin da zai taimakawa al’ummar Fulani domin mu samu mu zauna lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kasar nan. Inda duk ake noma a kashi 100 a ce za a baiwa Fulani makiyaya kashi 30, mu kuma mu tsaya daidai kashi 30 din, kashi 70 na manoma. A wani wuri kuma a kashi 100 a baiwa Fulani kashi 70, saboda ba a noman kirki a wajen, toh idan aka yi haka aka kebe mana irin wadannan wurare, za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan, ba wai wata jiha saboda kabilanci ta ce ta hana kiwo ba. Wannan ba zai kawo mana zaman lafiya ba.

Idan aka dauki dukkan kudin Najeriya aka baiwa ‘yan ta’adda Fulani wadanda shanun su suka kare a fadace fadace tsakanin Fulani makiyaya da manoma, babu abin da zai yi dangane da zaman lafiya Fulani makiyaya da manoma. Don haka idan ba wannan gyara aka yi ba, babu yadda za a cimma nasara.

Saboda haka gwamnati tayi abu mai dorewa kan zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here