Daliban Makarantun Firamare Dubu 220 Ne Ake Baiwa Abinci A  Filato-Dokta Sumaye 

0
778

Isah Ahmed Daga Jos

DOKTA Sumaye Hamza ita ce mai baiwa gwamnan Filato Shawara ta musamman, kan shirye shiryen tallafawa marasa galihu da gajiyayyu a Jihar Filato.

A wannan tattaunawa da ta yi da wakilinmu ta bayyana cewa, shirin nan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kirkiro na ciyar da daliban makarantun firamare a Najeriya, yana  ciyar da dalibai dubu 220 a makarantun firamare na Jihar Filato.

Har’ila yau ta yi bayani kan yadda shirin tallafin naira dubu 5 da ake baiwa gajiyayyu da shirin tallafin naira dubu 30 na N-Power da ake baiwa matasan da suka kammala manyan makarantu da shugaba Buhari ya kirkiro, suke tafiya a Jihar Filato.

Ga yadda tattaunawar ta kasance

GTK: Wadanne hali ake ciki dangane da shirin nan na ciyar da daliban makarantun firamare na gwamnatin tarayya a Jihar Filato?

Dokta Sumaye: Ya zuwa yanzu mun sami cigaba a wannan shiri na ciyar da daliban makarantun firamare a Jihar Filato, wanda gwamnatin tarayya ta kirkiro, domin yanzu muna ciyar da yara daliban makarantun firamare dubu 220 kuma muna da masu dafawa yaran abinci, sama da   3300. Wannan shiri na ciyar da daliban makarantun firamare, ana gudanar da shi ne a dukkan  makarantun firamare na kananan hukumomin  Jihar Filato 17.

GTK: Kamar wadanne irin abinci ne kuke baiwa daliban?

Dokta Sumaye: Muna basu abinci iri daban daban, kamar a ranakun litinin muna basu faten dankalin turawa da faten doya. Haka kuma kamar ranakun alhamis da talata muna basu kunun acca da ake hada masu da gyaro da gyada da waken soya duk wadannan abubuwa ne da suke gina jiki. Akwai kuma wani biskit da kamfanin Nasco yake yi mana, da aka sanya abubuwan da suke gina jiki da muke basu.

GTK: Ganin cewa a wasu wurare ana koke koke kan yanayin abincin da ake baiwa daliban nan, wadanne irin matakai ne kuke dauka wajen ganin masu dafa abincin nan, suna yin abincin kamar yadda aka tsara?

Dokta Sumaye: Muna da ma’aikatan da suke bi suna duba wannan abinci da ake baiwa daliban a makarantun firamare na Jihar nan. Muna da su a matakan makarantu kamar shugabannin makarantun da malamai da iyaye, inda muke karfafawa iyaye gwiwa kan su rika tabbatarwa yaransu suna cin abinci. Haka kuma a sashin ofisoshin da suke kula da makarantun firamare na kananan hukumomi, suma aikinsu ne su kula da abincin tare da tabbatar da yaran suna cin abincin. Haka a jiha ma muna da masu zuwa suna dubawa don ganin ana bin ka’ida wajen bayar da wannan abinci. Haka suma gwamnatin tarayya suna turo jami’ai da suke zuwa suna dubawa. Akwai matakai da dama da ake dauka wajen ganin an bi wannan tsari kamar yadda aka shirya shi.

Amma duk da haka ina kira ga iyaye da mutanen da suke cikin unguwannin da makarantun suke, su rika sanya mana ido su tabbatar cewa an baiwa yaran nan abinci. Duk inda suka ga ba a bayar da abincin nan, muna rokon su sanar damu domin mu dauki matakin gyara.

GTK: Dangane da shirin baiwa tsofaffi da gajiyayyu tallafin naira dubu 5 da shugaba Buhari ya kirkiro, shi kuma ina aka kwana a Jihar Filato?

Dokta Sumaye: A wannan shiri na tallafin naira dubu 5 shima zan ce mun cigaba a nan Jihar Filato. Domin a yanzu haka kananan hukumomi guda 6 na jihar nan, da suka hada da Bassa da Jos ta gabas da Kanke da Bokkos da Langtang da Wase, sun yi shekara guda ke nan suna karbar wannan tallafi. Kuma gidaje sama da guda dubu 30 da muka kididdige ne, suke karbar wannan tallafi a wannan jiha ta Filato, sannan ana yiwa wadanda suke karbar wannan tallafi bita kan yadda zasu sarrafa wannan tallafi da ake basu.

Bayan haka akwai wani kari kan wannan tallafi da ake bayarwa, a cikin wadannan kananan hukumomi guda 6. Wato idan aka je aka ga wata mace wadda take da ciki ko kuma take shayarwa,  idan aka tabbata  wannan mata taje asibiti ko  ta yi gwaji ko kuma ta kai danta rigakafi za a rika bata karin naira dubu 5, kan tallafin naira dubu 5 da ake bata.

Sannan kuma sauran kananan hukumomin jihar 11, muna nan mun  fara fadakar da su kan abubuwan da wannan shiri ya kunsa. Kuma mun  tantancewa al’ummomi da gidajen da suka cancanci a basu wannan tallafi. Don haka nan bada dadewa ba sauran kananan hukumomin  nan 11 za a sami wadanda za a rika basu wannan tallafi.

GTK: Idan muka koma ga shirin baiwa daliban da suka kammala manyan makarantu tallafi naira dubu na N-Power yaya wannan shiri yake tafiya a jihar Filato?

Dokta Sumaye: Wannan shiri na N-Power na baiwa daliban da suka kammala manyan makarantu tallafin naira dubu 30. A yanzu haka muna da mutane dubu 11 da suke cin gajiyar wannan shiri a Jihar Filato. Wadannan mutane a duk wata kowanne su yana karbar naira dubu 30. A kowanne wata wadannan matasa suna karbar tallafin naira miliyan 300 a nan Jihar Filato.

Akwai kuma shirin N-Power na koyon sana’o.i. A wannan shiri ana koyawa matasa sana’o’i daban daban kuma a  ana basu tallafin naira dubu 10 kowannensu. Haka kuma ana basu kayayyakin aiki domin su je suyi amfani da wadannan kayayyakin aiki, don su taimaki kansu su bude wararen sana’o’insu.

Bayan haka akwai tallafin bashi da muke bayarwa wanda bashi da ruwa. Wannan tallafi muna baiwa kungiyoyi daga naira dubu 50 zuwa naira dubu 100,000. Haka kuma muna baiwa kananan  ‘yan kasuwa bashin  naira dubu 10  shima babu ruwa a cikinsa.  Muna bin kasuwannan don mu sami kananan ‘yan kasuwa mu dauki sunayensu da bayanan su da hotinansu da hotinan sana’ar da suke yi, don mu basu wannan bashi.

GTK: To, a Karshe wanne sako ko kira ne kike da shi ga al’ummar Filato dangane da wadannan shirye shirye na tallafi da kuke gudanarwa?

Dokta Sumaye: To kira na ga al’ummar Jihar Filato shi ne idan gwamnati ta kawo tallafi, ko gwamnatin karamar hukuma ce ko gwamnatin jiha ko gwamnatin tarayya ce, idan aka kawo tallafi mutane su zo abin da basu gane ba, su yi tambaya. Saboda tallafin nan fa saboda ‘yan Najeriya aka yi shi, don haka kowanne dan Najeriya ya cancanci ya samu. Don haka idan mutane suka ji labarin ana bada tallafi su zo su yi tambaya, don a wayar masu da kai, domin su samu su ji gajiyar wannan shiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here