EFCC na binciken Dogara da Jibrin

0
801

Rabo Haladu Daga Kaduna

Hukumar EFCC da ke binciken masu yi wa tattalin arzikin kasa ta\’annati ta ce ta soma bincike kan badakalar cushen da ake zargin an yi a kasafin kudin kasa  na shekarar 2016.
Kakakin EFCC ya shaida wa manema labarai  cewa sun aika takarda ga majalisar inda suka nemi a basu wasu bayanai, sannan kuma za su gayyaci duk wadanda ke da hannu a lamarin domin bincikensu.
Wani fitaccen dan majalisar wakilai Abdulmumini Jibrin ne ya yi zargin cewa kakakin da wasu manyan \’yan majalisar sun yi cushen sama da N30bn a kasafin kudin shekarar 2016.
Ya bayyana haka ne bayan an cire shi daga shugabancin kwamitin kasafin kudi na majalisar, kodayake ya yi zargin cewa an sauke shi ne saboda yana adawa da shirin kafa dokar da za ta bada rigar-kariya ga shugabannin majalisar wakilan da ta dattawa.
Mista Jibrin ya kara da cewa \”Ina da shaidun da ke nuna cewa Dogara, da mataimakinsa Yusuf Lasun, da Alhassan Doguwa da Leo Ogor sun ware wa kansu 40bn a cikin 100bn da aka warewa gaba dayan majalisar dokokin tarayya ta kasa.
Rikici ya barke a majalisar wakilan
APC ta ja kunnen Abdulmumini Jibrin
Wannan batu dai ya janyo takaddama sosai a cikin majaliasar da ma kasar baki daya, inda wasu \’yan majalisar suka bukaci a yi bincike, suna masu cewa dukkan mutanen — Dogara da Jibrin — na bukatar a bincike su.
Da ma dai Abdulmumini Jibrin ya mika wasu takardu ga jami\’an tsaro, cikinsu har da EFCC da rundunar \’yan sanda da ta leken asiri, inda ya yi kira a binciki Yakubu Dogara da \’yan majalisar da yake zargi da hannu a badakalar.
\’Za su sha dauri\’
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya shaida cewa suna bincike a kan batun.
A cewarsa nan gaba kadan za su gayyaci shugaban majalisar wakilan da duk \’yan majalisar da ke da hannu a kan cushen.
Ya kara da cewa EFCC za ta hukunta duk dan majalisar da aka samu da hannu a cikin wannan badakala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here