Femi Gbajabiamila Ya Doke Abokin Takararsa Na Majalisar Wakilai Na 9

0
319

Daga Usman Nasidi.

AN bayyana sunan Femi Gbajabiamila na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin mutumin da aka zaba Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya.

Gbajabiamila, wanda ke wakiltar mazabar Surulere a jihar Legas, ya doke Umaru Bago daga jihar Naija, shi ma dan jam’iyyar APC.

Gbajabiamila ya samu kuri’u 281 yayin da Umar ya samu kuri’u 76. Sai dai yayin da jam’iyyar APC ta goyi bayan Gbajabiamila, ita kuwa PDP Bago ta nemi mambobinta su zaba.

Nasarar tasa na nufin APC ta samu abin da take so, bayan da Sanata Ahmed Lawan da Omo-Agege suka yi nasara a zaben shugabancin majalisar dattijai.

Zaben Gbajabiamila na zuwa ne shekara hudu cir bayan da ya sha kaye a hannun Yakubu Dogara a shekarar 2015 duk da cewa yana da goyon bayan jam’iyyar ta APC.

Femi Gbajabiamila, wanda lauya ne, yana da kwarewa a harkar majalisa kasancewar ya dade yana wakiltar mazabarsa a majalisar ta wakilai.

A shekara ta 2003 aka fara zabarsa a karkashin jam’iyyar AD kafin daga bisani ta rikide zuwa ACN da kuma APC daga baya.
Ya zama jagoran marasa rinjaye a majalisa ta bakwai zamanin shugabancin Aminu Waziri Tambuwal.

Sannan ya zama na masu rinjaye a majalisa ta takwas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here