Gbang Gwom Jos Ya Gargadi Lalong Kan Daga Darajar  Wasu Masarautu

0
365

Isah Ahmed, Daga Jos.

GBANG GWOM Jos Jacob Gyang Buba ya gargadi gwamnan Jihar Filato Simon Lalong kan ya dakatar da daga darajar wasu masarautu guda biyu zuwa masu daraja ta daya, da ya yi a masarautar Gbang gwom na Jos, domin gujewa sake fadawa wani sabon  rikici a Jihar.

Gbang gwom na Jos ya yi wannan gargadin  ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin ranar kabilar Birom da aka gudanar a garin Jos.

Gbang gwom na Jos wanda shi ne shugaban majalisar sarakuna ta jihar Filato, ya yi bayanin cewa a tarihi bai taba ganin inda gwamnati tayi wani gyara kan iyakokin wasu kabilu da suke zaune lafiya ba.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Jihar Filato ta bada sanarwar cewa ta kirkiro masarautu masu daraja ta daya a kananan Hukumomin Jos ta Arewa da Riyom.

Wannan mataki da gwamnatin ta dauka ya rage karfin Gbang Gwom na Jos,  inda yanzu aka bar shi da kananan hukumomi guda biyu kadai, wato Jos ta kudu da Barikin Ladi maimakon kananan hukumomi guda hudu da suke karkashinsa ada.

Sanarwar tayi bayanin cewa Sarkin Ganawuri Attah Aten ne sabon sarkin majalisar sarakuna ta Riyom a yayin da Sarkin Anaguta ne shugaban majalisar sarakuna ta Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Gbang gwom na Jos ya yi bayanin cewa ya kamata gwamna Lalong ya ya yi amfani da dokar mallakar kasa.

Ya ce kasar nan tana da dokar mallakar kasa wadda ta baiwa asalin ‘yan kasa mallakar kasa.

‘’ A Najeriya kasa mallakar al’ummomi da iyalai da sauran jama’a ne, don haka muna kira ga gwamnatin Filato ta guji aikata abin da zai sanya a sake fadawa wani sabon  rikici a jihar.

‘’zamu yi zama da gwamnati mu wayar masu da kai kan wannan al’amari, muna fatar gwamna zai sanya kunne ya saurare mu, domin ganin ya yi gyara kan wannan al’amari. Domin babu wanda ba ya  kuskure’’.

Ya bayyana cewa dukkan rahotanni  kwamitocin binciken rikicin Jos da aka kafa a shekarun baya, sun yi matsaya kan cewa garin Jos mallakar kabilun Afizere da Anaguta da Birom ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here