Gidauniyar Annur Ta Ciri Tuta Wajen Kyautata Rayuwar Al’umma

0
163

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

SAKAMAKON kafa gidauniyar Annur Kibiya, al’umomi masu tarin  yawa sun amfana daga  kyawawan tanade-tanaden gidauniyar kuma ta fannoni daban-daban wadanda suka hada da harkar samar da  ruwan sha kyauta, da bunkasa ilimi da kuma yunkurin kawo sauyi a tsarin karatun allo.

Dakunan karatu a makarantar allo ta Kura domin inganta karatun allo a zamanance.

Sannan bisa yadda gudauniyar ta ke gudanar da aiyukanta, akwai kyakkyawan zato cewa nan gaba kadan, Annur Foundation Kibiya zata zamo daya daga  cikin gidauniyoyi da suka yi fice wajen taimakawa al’u.ma domin Allah musamman ganin yadda ta ke aiwatar da aiyuka masu inganci da aminci domin a dade ana amfanar su.

Makarantar Koyar da marayu ta Kibiya da Annur ta gina.

Haka kuma gidauniyar ta Annur tana kara bullo da tsare-tsare na kyautata rayuwar al’umma ne  bisa yin la’akari da bukatun jama’a a birane da kuma yankunan karkara, domin tallafawa kokarin gwamnati na bunkasa rayuwar al’uma kamar  yadda ake  gani a halin yanzu.


Dakunan kwanan almajirai a makarantar allo dake Kura wadda gidauniyar Annur ta Gina.
Dakunan karatu a makarantar allo ta Kura domin inganta karatun allo a zamanance.

Jagoran gidauniyar, Dokta Aliyu Musa Aliyu Kibiya ya bayyana cewa gidauniyar Annur zata ci  gaba da aiyukan alheri ga al’uma, tareda kyautata yanayin zamantakewa ta fuskar samar da ruwa da ilimi da kuma yunkurin samar da wani guri na kula da lafiya kyauta kuma domin Allah wanda shine manufar kafa gidauniyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here