Gwamna Udom Emmanuel Ya Nada Emmanuel Ekuwem Sakataren Gwamnati

0
258

Daga Mustapha Imrana Abdullahi.

GWAMNAN Jihar Akwa Ibom Mista Udom Emmanuel ya sake nada Dakta Emmanuel Ekuwem a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar.

A bisa bayanan da suke fitowa sun bayyana cewa an yi hakan ne domin a samu ci gaba da aiwatar da ayyukan Gwamnati kamar yadda ya dace.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da babban Mai magana da yawun Gwamnan Ekerete Udoh, ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a birnin Uyo.

Wadansu al’umma da wakilin mu ya ji ta bakin su cewa sake nadin Sakataren Gwamnatin ya dace kwarai bisa la’akari da irin kwazon aikin da yake da Shi ba dare ba Rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here