Hada Hanu Da Jami’an Tsaro Ne  Zai Magance  Kashe Kashen Da Ske Yi A Zamfara – Adam Mai Yadi

0
455

Isah Ahmed Daga Jos

SARKIN Yamman Hakimin Akuzo da ke masarautar Wonaka ta gabas  a Karamar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Adam Mai yadi Jos, ya bayyana cewa al’ummar Jihar Zamfara su baiwa jami’an tsaro goyan baya tare da hadin kai ne kadai zai magance kashe kashen da ‘yan ta’adda suke yi, a Jihar.Sarkin Yamman ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Ya ce ya kamata masu ruwa da tsaki kan harkokin mulki a Zamfara da sauran al’ummar jihar su kawar da banbancen siyasa, su hada kai da jami’an tsaro kan yaki da miyagun da ake yi a jihar,  don a sami nasarar kawo karshen kashe kashen bayin Allah da ake yi a jihar.

Sarkin Yamman ya yabawa jami’an tsaron  kan nasarar da suka samu a kwanakin baya, inda suka kashe ‘yan ta’adda sama da guda 150.

Ya koka kan karuwar rashin tsaron da ake fama da shi a jihar. Ya ce yana daya daga cikin wadanda wannan matsala ta rutsa da su. Domin kwanakin baya ‘yan ta’addar sun kashe kaninsa mai suna Alhaji Abdullahi kuma ya rasu ya bar ‘yaya 19.

Har’ila yau ya ce a kwanakin baya ‘yan ta’addar sun aukawa kauyensu, sun kashe mutane 18. Ya ce wannan babbar barazana ce ga rayuwarsu. Don haka ya bukaci gwamnati ta taimaka masu da jami’an tsaro.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here