Hayakin Janareto Ya Kashe Mutane 10 A Jihar Imo

0
211

Musa Muhammad kutama, Daga kalaba.

HAYAKIN janareto ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan biki mutum goma ranar litinin data gabata yayin da kusan mutum ashirin ke kwance a asibiti mutu-kwaikwai-rai kwai bayan da suka shaki hayakin janareto da akewa lakabi “nafi makwabcina” saboda yawan samun daukewar wutar lantarki da ake fama dashi a kasar nan domin ya samarwa ‘yan bikin haske kada su kwanta cikin duhu.

Wannan lamari ya faru a kauyen Umuomomo Mbiereri, dake karamar hukumar Mbatoili jihar Imo.

Mazauna kauyen sun sanarwa wakilin mu cewa sama da mutum talatin ne suka suma aka kaisu asibitoci daban daban na karamar hukumar, wasu kuma asibitin Ikeduru aka kai su suna kwance
mutu-kwaikwai-rai kwai likitoci na kokarin ceto rayuwar su .

Majiyar labarin ta bayyana cewa a gida da aka daura auren ne lamarin ya auku yayinda aka kare shagulgula inda wasu daga cikin dangin amarya da angon suka zo daga Aba jihar Abiya suka yanke shawarar kwana a kauyen washe gari su tafi.

Bayan wayewar gari safiya ne akaga baki basu fito daga daki ba aka kwankwasa ana zaton ko makara suka yi inda daga karshe dai aka balle kofar dakin aka ga mutanen kwance ba rai har su goma daga nan ne aka kira mutane domin su kawo dauki ga masu sauran numfashi kuma aka garzaya dasu asibiti.

Basaraken kauyen mai suna Martin Ezurike, ya sanarwa manema labarai cewa shi ne ya bayar da motarsa da aka kwashi wadanda abin ya rutsa dasu zuwa asibitocin, kana ya kara da cewa an kunna janareton ne tun daren lahadi aka ajiyeshi a dakin dafa abinci inda hayakin ya rika shiga dakin da suke da yake dakin dafa abincin yana kusa da dakin da bakin suka kwana.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo Rabi’u Ladodo ya shaidawa cewa ya bayar da umarnin a gaggauta yin bincike game da abinda ya farun.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa “janareton yana dakin dafa abinci, su kuma bakin suna dakin su daban kusa da dakin dafa abincin tagogin dakin a rufe amma dai ko ma yaya aka yi mutuwar mutum goma akwai ayar tambaya don sai anyi bincike tukuna a gano musabbabi don haka na bayar da umarnin ayi bincike sahihi domin gano inda aka samu matsala.

Ya zuwa rubuta wannan labari mutum ashirin ne ke kwance a asibitin Ikeduru likitoci na bakin kokarin suga sun ceto rayuwar su.

Hakazalika, shugaban asibitin Ikeduru Dokta Austin Agbahiwe ya tabbatar da mutuwar mutum uku lokacin da aka kawo majinyatan asibitin kafin ma ayi musu wani aiki na gaggawa sauran kuma an sanya musu na’uran taimaka musu yin numfashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here