Jami’an EFCC Sun Kama Wasu Matasa 7 Yan Damfara A Yanar Gizo

0
221
Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna.
OFISHIN shiyyar kaduna na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa sun yi nasarar kama wadansu mutane bakwai da suka hada da mace daya da zargin  laifin damfara a yanar Gizo.
A ranar Juma’a 21, ga watan Yuni 2019 ne dai ofishin ya yi wannan nasara kama mutanen.
Wadanda da aka kama da laifin zargin yin damfarar matasa ne yan shekaru ashirin zuwa talatin da uku an kuma kama su ne da misalin karfe biyar na safiya a wani wurin da Suka kama haya da ke kan titin Ijejirika Becky, Karu, cikin Jihar Nasarawa.
Wadanda ake zargin da ake kira da “yahoo boys” da suka kasance tare da wata mace daya suna aikata ayyukan nasu ne a wuraren Maraba, Nyanya da wajen Karu da ke cikin Jihar Nasarawa da kuma babban birnin tarayya Abuja.
An dai samu nasarar kama sune bayan da aka samu bayanan sirri a kan ayyukansu.
Daya daga cikin wadanda ake zargin da ya bayyana da sunan Injiniya mai aiki da kamfanin “Exxon Mobil” sauran kuma amfani da katin shaida na jabu suna damfarar jama’a da ke ciki da wajen Najeriya.
Wadanda ake zargin sun hada da Peter Olu Tsetimi, Ogunbiyi Adekunle A, Emuze Omosigho Emmanuel, Isaac Daro Obozokhai.
Sauran sun hada da Samuel Nana Kofi Eruese, Edward Yusuf da Peace Manayin. Abubuwan da aka samu a tare da su sun hadar da manya manyan Agoguna a sarkoki da wayoyin salula na hannu masu tsada kamar su iPad,kwanfutocin hannu da sauran abubuwa da Suka damfari jama’a.
A nan dai ana ci gaba da gudanar da bincike za kuma a yi amfani da abubuwan da aka samu a wajen su domin ci gaba da gudanar da binciken kwakwaf.
Za a kuma gabatar da su a gaban kuliya manta sabo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here