Ku Daina Garkuwa Da Mutane Ko Nu Taru Mu Yi Maku Addu’a – Sheikh Jingir

0
409

Isah Ahmed, Daga Jos.

SHUGABAN majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga matasa masu mummunar dabi’ar nan ta garkuwa da mutane a kasar nan, da su tuba su bari ko kuma al’ummar kasar nan su taru su yi masu mummunar addu’a.

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude wani sabon masallaci da aka gina, a unguwar Zinariya da ke garin Jos.

Ya bayyana cewa matasa kowa ya nemi sana’a ya guji aikata sana’ar garkuwa da mutane, domin daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu an kashe daruruwan matasa masu irin wannan mummunar sana’a.

Ya ce ‘’Muna kira ga matasan da suka shiga wannan mummunar sana’a su tuba, su bari. Idan kuka ce ba zaku tuba ku daina ba, zamu hada kai da junanmu mu yi ta yi maku miyagun addu’o’i dare da rana’’.

Sheikh Jingir ya yabawa al’ummar wannan unguwa ta Zinariya, kan yadda suka yi gine ginen gidaje a wajen.

Acewarsa, kamar shekaru 22 da suka gabata ya bayar da shawarar cewa ya kamata mutanen suje su sayi filaye a wannan tsauni na Zinariya su gina gidaje.

Ya yi kira ga al’ummar wannan unguwa da su taru su raya wannan masallaci.

Shima da yake jawabi a wajen shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala reshen Unguwar Zinariya Alaramma Malam Abdurrahaman Ahmad ya bayyana cewa shi dai wannan sabon masallaci da aka gina, masallaci ne na salloli guda 5 amma mai kama da masallacin juma’a, domin yana da fadi.

Ya yi kira ga masu hanu da shuni da su yi amfani da dukiyarsu wajen aikata irin wadannan ayyuka.

Tun da farko a nasa jawabin wanda ya gina wannan masallacin, Alhaji Umaru Zubairu Lalu ya yi godiya ga Allah da ya bashi damar gina wannan masallaci.

Ya bada tabbacin cewa da yardar Allah zai gina azuzuwan koyon karatun Alqura’ani a wannan masallaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here