Matan Jihar Kano Suna Godiya Ga Gwamna Ganduje – Inji Hajiya Alpha Dambatta

0
519

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

MAI baiwa shugaban karamar hukumar Dambatta shawara kan al’amuran mata, Hajiya Alpha Abdu Usman Dambatta ta ce matan jihar kano zasu ci gaba da yin godiya ga gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda damar da yake basu domin bada tasugudummawar wajen ciyar da jihar gaba.

Gwamnan Jihar KANO Dakta Umar Abdullahi Ganduje

Ta yi wannan tsokaci ne cikin tattaunawar su da wakilin mu a Dambatta, inda ta sanar cewa gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta cancanci yabo da fatan alheri saboda sanya mata da ake yi cikin shirye-shiryen ta na jagorancin al’uma, sannan tace ana kara bullo da hanyoyi masu tarin yawa domin ganin matan jihar kano suna cikin yanayi mai kyau na zamantakewar yau da kullum.

Hajiya Alpha Dambatta, wadda aka fi sani da “Maman Maja” , ta bukaci daukacin matan jihar kano da su ci gaba da yin biyayya ga gwamnatin ta Ganduje saboda kokarin da take yi wajen bunkasa rayuwar mata da lalubo Karin hanyoyi na taimaka masu musamman ta fannin kula da lafiya da koya masu sana”‘oi da basu jari da kuma baiwa ilimin mata muhimmanci.

Bugu da Kari, Hajiya Alpha Abdu Usman Dambatta ta yi amfani da wannan dama wajen jinjinawa uwargidan gwamnan jihar Kano Hajiya Dokta Hafsat Absullahi Umar Ganduje saboda shawarwari nagari da take baiwa maigidanta wajen kyautata rayuwar Mata da yara kanana kamar yadda ake gani a fadin jihar, inda kuma tayi fatan alheri ga gwamna Ganduje bisa sake rantsar dashi da aka yi a matsayin gwamnan kano Karo na biyu.

A karshe, ta yi alkawarin ci gaba da bada gudummawar ta ga gwamnati mai ci tare da hade kan mata wajen ganin jihar kano ta Kara bunkasa ta kowane fanni a birni da kuma yankunan karkara batare da nuna gajiyawa ba, inda kuma ta godewa al’umar jihar kano saboda sake baiwa gwamna Ganduje goyon baya karo na biyu da aka yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here