Muryar Talaka Da Rundunar Adalci Sun Bukaci A Sake Nada Solomon Dalung Minista

0
332

Isah Ahmed, Daga Jos.

KUNGIYAR Muryar Talaka ta kasa da Kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Filato da Kungiyar Rundunar Adalci reshen Jihar Filato, sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada tsohon ministan wasanni da matasa, Barista Solomon Dalung a matsayin  minista. Kungiyoyin sun bayyana wannan bukata ce a wani taron ‘yan jarida da suka kira, a garin Jos babban birnin Jihar Filato.

Da yake jawabi ga ‘yan jarida a madadin kungiyoyin, Babban Sakatare Kungiyar Muryar Talaka ta kasa Kwamared Bashir Dauda Sabo Unguwa Katsina, ya bayyana cewa sun kira taron ‘yan jarida ne, domin su yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan wadanda ya kamata a nada ministoci.

Ya ce  a matsayinsu na ‘yan wadannan kungiyoyi  suna ganin cewa cikin ministocin shugaba Buhari da suka sauka, akwai wadanda suka yi abin azo a gani. Kuma daga cikin wadanda suka yi abin azo a   gani, akwai tsohon ministan matasa da wasanni Barista Solomon Dalung.

Ya ce suna ganin cewa irin abubuwan da Barista Dalung ya yi, lokacin da yake kan wannan kujera, ya kamata shugaban kasa ya kara bashi dama, domin yazo ya cigaba da ayyukan da ya fara.

‘’Na farko da aka nada wannan mutum ya yi kokari ya kawo canji a hukumomin wasanni na Najeriya. Inda aka zabi shugabanni  wadannan hukumomi. Kuma sakamakon wannan kokari da ya yi kungiyoyin wasanni na wadannan hukumomi  sun shiga gasa iri daban daban, har ya zuwa gasar wasanni na duniya  suka taka mahimmiyar rawa. Suka ciwo wa Najeriya lambobin yabo. Wanda ada a Najeriya ana maganar kwallo ne kawai. Amma sakamakon wannan canji da aka samu a wadannan hukumomi yanzu ana maganarsu a  gida Najeriya da kasashen waje’’.

Kwamared Bashir ya yi bayanin cewa  lokacinsa ne saboda gudunmawar da yake bayarwa Najeriya taje wasan cin kofin kwallon kafa na duniya, a shekara ta 2018 a kasar Rasha ta nuna bajinta.

Haka kuma ya ce a lokacinsa ne  ‘yan kungiyar kwallon kafa ta matan Najeriya suka je suka ciwo kofin Duniya.

Har’ila yau ya ce an dade ba ayi wasannin al’adun gargiya na kasa a Najeriya ba. Amma lokacinsa  ya yi kokari gwamnatin tarayya ta shirya wannan wasa a  Abuja. Kuma a lokacinsa ya ya gina filayen wasanni da dama a Najeriya.

Ya ce ya kyautatawa kungiyoyin matasa tare  da   koyawa matasa sama da 1500 sana’o’i daban daban a Najeriya.

Ya ce shi mutum ne mai son hadin kan kasa. Kuma  bai son nuna banbancin addini ko kabilanci. Don haka yana da kyau a bar shi a cikin wannan gwamnati.

Ya ce babu shakka shugaba Buhari yana bukatar mutane irinsu Barista Solomon Dalung,  a cikin gwamnatinsa saboda irin gudunmawar da yake bayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here