Sarkin Saminaka Ya Nada Sabon Turaki Babba Na Saminaka

0
240

Isah Ahmed, Daga Jos.

MAI martaba Sarkin Saminaka da ke Jihar Kaduna Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada Abdurrahaman Ado Abubakar Yango a matsayin sabon Turaki babba na masarautar Saminaka tare da nade naden  wasu sarautun, a karshen makon da ya gabata a fadarsa da ke garin Saminaka.

Sauran wadanda aka nada din sun hada da Sani Musa Sani a matsayin Turakin  Saminaka da Usman Musa Sani Yariman Saminaka da Musa Shehu Sani a matsayin Dan’amar Saminaka da dai sauransu.

Da yake jawabi a wajen Mai Martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani bayyana cewa an nada wadannan matasa ne saboda ganin cancantarsu. Don haka  ya yi kira ga wadanda aka nada, su tsaya wajen ganin sun yiwa  wannan masarauta aiki da kasa baki daya.

Ya yi  kira ga al’ummar  masarautar  su cigaba da zaman lafiya da junansu kamar yadda suka saba.

Har’ila yau ya yi kira ga al’ummar masarautar su cigaba da rungmar sana’ar  aikin noma musamman ganin sunan da suka yi a duniya ta hanyar wannan sana’a.

Da yake zantawa da wakilinmu Sabon Turaki babba na Saminaka Abdurrahaman Ado Abubakar Yango ya mika godiyarsa ga mai martaba Sarkin Saminaka kan wannan sarauta da aka nada shi domin ya bada gudunmawarsa ga masarautar.

Har’ila yau ya mika godiyarsa ga iyaye da  ‘yan uwana  kan goyon bayan da hadin kan da suka bashi kan wannan sarauta.

Daga nan ya bayar da tabbacin cewa da yardar Allah zai bayar da gudunmawarsa  ga masarautar kamar yadda ya ga mahaifinsa yana yi, lokacin da yake raye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here