Zan Bunkasa Ilimi Da Koyawa Matasa Sana’o’i A Jos Da Bassa – Haruna Maitala

0
329

Isah Ahmed , Daga Jos.

ZABABBEN dan majalisa wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato, Alhaji Haruna Maitala Jingir ya bayyana cewa zai mayar da hankali wajen bunkasa ilmi da koyawa matasa sana’o’i a mazabarsa ta Jos da Bassa. Alhaji Haruna Maitala Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Jos.

Ya ce zai mayar da hankali wajen ganin  yara sun  yi karatu a wannan mazaba kuma zai taimaka wajen ganin matasan wannan mazaba sun koyi sana’o’in hanu kamar gyaran motaci da walda da kafinta da dai sauransu.

Ya ce babu shakka idan aka bunkasa ilmi da samar da ayyukan yi ga matasa, za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan mazaba.

Har’ila yau ya yi bayanin cewa zai hada hanu da jami’an tsaro da sauran al’ummar wannan mazaba,  wajen ganin an sami tabbatatcen zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan mazaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here