Manoma Sun Koka Game Da Faɗowar Jirgi A Gonarsu

0
7891

MUHAMMAD SHAFI’U SALEH, Daga Yola

A YANZU haka, manoman da jirgin gwamnan Jahar Taraba Ɗanbaba Ɗanfulani Suntai ya faɗi masu a gonaki sun koka game da irin asarar amfanin gonar da faɗuwar jirgin ta haifar inda suka ce ko rabin abin da suke samu duk shekara ba za su samu a bana ba.

Zira Kuji mai shekara 40 da Misis Godiyya Dauda mai shekara 32 su ne waɗanda jirgin ya faɗo masu a gonakinsu sun nuna damuwa don kuwa kamar yadda suka bayyana suna daga cikin mutanen da ambaliyar ruwa ta cinye wa gonaki sai kuma ga wannan matsalar ta faɗuwar jirgi wanda suka ce ya yi kaca-kaca da gonakinsu.

Zira ya ci gaba da cewa, a shekaru biyun da ya yi yana noman gonar yana samun amfanin gona fiye da buhu 52 amma sakamakon matsalar haɗarin da jirgin ya yi, gonar ba zai samu ko da rabin abin da yake samu duk shekara a bana ba.

Haka ita ma Misis Godiya ta ce tana samun amfanin gona buhu 21 a tsakanin masara da wake amma babu alamun samun ko da rabin abin da ta samu a bara, don kuwa ta ce bayan jirgin ya faɗi ya kuma ja a gonarta sannan kuma jama’a masu zuwa kallo suna tattake ɗan amfanin da ya saura.

Don haka suka yi fatar samun sauƙi ga waɗanda haɗarin ya rutsa da su kana suka buƙaci gwamnatin jahar da ta duba masu bisa asarar da suka tafka a haɗarin kuma suna cikin mutanen da suka sami matsalar ambaliyar ruwa a jahar amma babu sunansu daga cikin jerin sunayen da za a tallafa masu.

Gaskiya Ta Fi Kwabo dai ta gano cewa, asalin gonakin mallakar shugaban jam’iyyar PDP ta ƙasa, Alhaji Bamanga Tukur ne inda suke bai wa manoma haya suna nomawa. Zira ya ce sun biya kuɗin gona ga matsalar ambaliyar ruwa yanzu kuma ga wannan matsalar da ta yi masu kaca-kaca da gona.

Har zuwa wannan lokaci da aka haɗa wannan rahoto dai ba wani matakin da hukumomin da abin ya shafa suka ɗauka game da koke-koken da kuma halin da manoman suke ciki game da asarar kayan gona da faɗuwar jirgi a gonakinsu ya janyo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here