ARZIKIN MALAMIN ADDINI

0
1512

Daga MUHAMMAD SABO WUSHISHI

IDAN Allah Ya yi wa malamin addini arziƙi yana da abin buƙata kuma yana ibada ba wanda ya fi shi jin daɗin duniya domin ba a ɗora masa mulki ko neman dukiya da tattalinta ba, ba a kuma ba shi ilimin da wani zai tilasa masa yin aiki ba, balle a ce ana cancanza masa wurin zama da tilasta masa biyayya ga wanda duk ba ƙarƙashinsa yake ba.

Amma in har Malamin addini ba shi da abin buƙata na rayuwa ko ya kasance ba ya yin aiki da iliminsa na addini babu wanda zai fi shi faɗawa ga damuwa ko ƙasƙanci, sai wanda bai kasance yana da imanin da Allah da manzonSa ba.

Domin wanda ya kasance bai yi imani da Allah ko littat-tafanSa, ko manza-ninSa ko shi ne Mahaliccin kowa da komai ba, ko ba Allah ne Ya cancanci a yi wa biyayya ba, ya ƙulla ɗaya daga cikin waɗannan balle duka, ba a fi shi taɓewa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here