Gwamna Suntai Ya Bayyana A Karon Farko

0
1222

GWAMNAN  Jahar  Taraba, Ɗanbaba Ɗanfulani Suntai, ya yi bayyanarsa ta farko a cikin hoto ba a bayyane ƙarara ba, tun bayan da ya sami haɗarin jirgin sama a ranar 25 ga watan Oktoba a kusa da filin jirgin sama na Yola, hedikwatar Jahar Adamawa.

Rahotannin da muka samu kamar yadda jaridar “The Nation” ta bayyana tuni an sallame shi daga asibitin ƙasar Jamus inda likitoci suke yi masa aikin karairayewar da ya samu da yawa a jikinsa.

A cikin wani hoton da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya bayyana a fili, Gwamna Suntai ya bayyana a fuskar baƙiƙƙirin ba kamar yadda aka saba ganinsa ba.

Yana riƙe da yaro wato jaririn da matarsa, Hajiya Hauwa ta haifa masa a ranar 6 ga watan Disamba duk a ƙasar Jamus, yana kallon na’urar ɗaukar hoto kai tsaye, matarsa kuma na riƙe da sauran.

Gwamna Ɗanbaba Ɗanfulani Suntai na sanye da farar riga (shirt” kansa da fuskarsa a aske. A cikin hoton da aka ce an ɗauka a cikin wani kantin sayar da abinci da ba a bayyana sunansa ba, Gwamnan na zaune a kan wata baƙar kujera da ya bambanta da saura a cikin kantin sayar da abincin. A gabansa da akwai kwanon abinci da aka ci rabin kwanon, sai kofin ruwa da abin zuba gishiri.

Wani mutum da ke zaune kusa da shi daga bayansa na sanye da baƙaƙen kaya kamar yadda jami’an tsaron Najeriya ke yin shigarsu ta aiki, amma fuskarsa na’urar ɗaukar hoto ta kare ta.

Amma ba a bayyana dalilin da ya sa aka bayyanar da hoton ba, domin lamarin ya zo ne lokacin da ake tsakiyar yaɗa bayanan da ke cewa, Suntai na cikin halin da ba zai iya moriya ba har abada.

Ɗan majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha da ke wakiltar mazaɓar Taraba ta Kudu abokin Suntai na kusa, haihuwar tagwayen da aka yi a gidan Suntai ya zamo wani babban al’amari na farin ciki musamman saboda sallamarsa daga asibitin da aka yi.

“Tafiyar matar Suntai ƙasar Jamus an yi shi ne domin ta taimaka wa mijinta sai lamarin ya sauya inda aka shirya za ta tafi ta haihu a ƙasar Amurka. Sakamakon haihuwar waɗannan ‘yan biyu, ‘ya’yansu sun zama guda 5 ke nan, mata 4, namiji 1 (yana ɗaya daga cikin jariran da aka haifa yanzu). Sanata Bwacha ya ce, gwamnan ba sauri yake ba ya dawo gida, domin yana son sai ya kammala warwarewa baki ɗaya. Ya ƙara da cewa, gwamnan ya tabbata mai riƙon gwamna Garba Umar zai iya tafiyar da komai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here